Wednesday, 6 July 2016

Gaskiyar Maganar Da El-Marzuk Yayi Akan 'Yan Social Media

Ako da yaushe labari wanda yake na shin fuska ya fi daukar hankalin jama’a da al’umma. To amma manufa da tunanin sarrafa labari ya sha banban da dama.

Katsina Reporters ta buga wani labari mai take “Ku buge da Gura idan kun gansu” wanda a yarda suka baiyana cewa “Attorney General” na Katsina Elmarzuk ya furta a yayin da Gwamna Aminu Masari ya gaiyatu ‘yan Social Media buda baki  Azumi a gidan gwamnati.
To Nidai a matsayina na shugaban Cliqq Magazine Nayi Allah wadarai da Hotun (picture) da Katsina reporters tayi amfani wajen buga labarin ta ba tare da daukar izinin  (permission) mu ba.

Sannan kuma na hallarci wannan taro da akayi da ‘yan Social Media wanda Alh Usman Ventures yayi jagora, Usman Ventures yayi bayani matukar bayani wanda yayi kira ga Gwamna Masari da kamanta adalchi a mulkin sa, Sannan kuma ya kara kira ga ‘yan Social Media da suji tsoron Allah akan irin maganganu masu muni ko korafi mara amfani.
Daga nan Shugaban Katsina State Social Media Organisation Dahiru Mani yayi bayani mai kyau a inda yayi ma Gwamna Magana akan Albashin ‘yan kananan hukomumi da kuma akwatin “suggestion Box” da gwamnati tasa a wurare da kauyuka a Katsina.


Ana shi jawabin, Elmarzuk(Attorney general” yayi Magana ne akan halaiyar gwamna Masari ga yadda yake da hakuri da kauda ido ga masu mashi shin fuska, da zagi wanda basu mashi adalchi . Sannan ya kuma yi Magana akan masu zagin matan gwamna, ko ayi amfani da hotunan su don shin fuska wanda yace ba ruwan mabiya da “personal Life “na Gwamna Masari.

Sannan ya kara da cewa ba za su yadda da irin hakan ba ga yadda ake zagin iyalen su wanda bai da kyau ko a musulunci. Ya kare maganar shi da cewa idan kuma masu zagin iyalen su hakanan don iyayen gidajensu suna sa su don aikata hakan, to za su fara daukan matakan Shari’a akan masu yin haka.

Ana ci jawabin, Gwamna Masari yayi Magana sosai akan masu zagin shi ko iyalen sa. Wanda ya baiyana yace sau dayawa ana mashi “text message” na zage zage wanda yace idan mutum yayi nafarko, sai ya kauda ido, idan yayi na biyu ya kuma kara har sau ukku, to yana da hurumin yasa hukuma ta jama masu layi don kada su koma.


A karshe gaskiyan Magana shine babu inda El-marzuk yace Ku bege da gora idan kun gansu, wannan kage ne da kuma raunin kafofin labaran mu na zamani.

2 comments:

  1. Muda aka kulle damu dakai aciki wajen taro kuma ni dakai ko yasan abun da akayi wajen sai kazo kana karya ta abunda kaji da kunne ka don baka tsoron Allah. i will reveal the videos ko dan na gasgata wannan statement inna ka.

    ReplyDelete
  2. we are disappointed in you. Ranar Sallah amma kafito kayi ma mutane karya. ance dai idan zaka fadi zance ka fadi zance na gaskiya

    ReplyDelete