Tuesday, 25 July 2017

Sarkin Sullabawan Katsina Ya Nada Ismail Usman Yandaki Garkuwan Kaita


Sarkin Sullubawan Katsina Alh Abdulkarim Kabir Usman ya nada Hon. Ismail Yandaki a matsayin Garkuwan Kaita.
Alh. Abdulkarim Kabir yace wannan mukamin Garkuwar Kaita sarauta ce mai matukar tarihi, wanda ganin irin rawar da Ismail Usman Yandaki yake takawa don ganin cewa ya taimaki al’aummar karamar hukumar Kaita.
Ya ce Ismail Usman Yandaki ya taka rawa iri daban-daban wajen zama garkuwa ga talakawan garin kaita da kewaye wajen bada tashi gudunmuwar tallafi a matsayin shi na mai taimaka wa  sanata Umar Kurfi Nzeribe.
Hon. Ismail Usman Yandaki shine Babban mai taimaka ma sanata Umaru Kurfi Nzeribe wajen tafiyar da al’amurranshi na yau da gobe.

No comments:

Post a Comment