Monday, 4 July 2016

Yaro Dan Shekara Goma Sha Biyar (15yrs) Ya Kashe Kanshi A Layout, Katsina

Emanuel Kenan Tare Da Kanwanshi
A ranar Asabar 2/07/2016 da ta gabana, wani yaro mai suna Emanuel ya kashe kansa da kansa a layout, layin gidan Rahusa da ke cikin brinin Katsina.

Cliqqmagazinehausa.blogspot.com tayi tattaki zuwa gidan yaron don samun yadda asalin labarin yake.

Wakilin mu ya isa gidan su yaron wanda ya samu ganawa da mahaifiyar sa, amma a lokacin mahaifin yaran ya tafi asibitin da aka aje gawar yaron.

Inda Emaneul Ya Hange kanshi
Kamar yadda mahaifiyar yaron ta zaiyanama wakilinmu shine, “A ranar Asabar da safe Yaranta Emaneul yace zai tafi Church domin koyan waka irin ta churchi (choir practice), gashi kuma na riga na kusa gama abinchi, sai na umurce shi daya tsaya sai ya ci abinci kafin ya tafi, saboda duka duka shekarar shi goma sha biyar (15yrs). Saboda irin son addinin shi yasa ya fusata ya shiga daki ya kulle kofa, jim kadan kenan bayan nagama dafa abincin na umurci kannan sa dasu kira ci domin yazo yaci abinchi, da suka shiga daki sai suka ganshi kwance kamar yana bacci, su kadawo su kace min ai bacci yake yi wanda nakara cewa su je su kirashi yazu ya ci abinci, su ka kara dawowa suka ce man Emanuel fa ya tashi fa a tsaye harshen na waje fa, sai na maza na shiga a inda na ga ya sargafe wuyanshi a jikin igiyan wando (belt) a kan tebur harshe waje, hakura sun datse harshen shi, a lokacin dana shigo dakin yariga ya mutu”.
Kofar Shiga Dakin Mahaifiyar Emanuel 
Mahaifiyar Emanuel mai suna Juyana, tace yaron ta mai son addini ne sosai, kuma bai taba yimata koke ba akan wani abu dake damun shi ba, ko wani dake mashi barazana.

Mutuwar Emanuel dai ta zama abun mamaki yadda yaro dan shekara Goma sha Biyar (15Yrs) ya kashe kansa da kanshi har ya mutu ko shure shure ba’a jiba yanayi ba.

Gate Din Shiga Compound Din Su Emanuel Kenan Wanda ke kan Titin Gidan Rahusa, Layout Katsina
Wakilin Cliqqmagazinehausa.blogspot.com ya samu labarin cewa ma’aikatan Yan sanda tuni sun zo suyi bincike a inda suka dauke Igiyar wandon yaron (belt) da Kuma teburin daya hau ya taka wajen Kashe kansa.

No comments:

Post a Comment