Ako da yaushe labari wanda yake na
shin fuska ya fi daukar hankalin jama’a da al’umma. To amma manufa da tunanin
sarrafa labari ya sha banban da dama.
Katsina Reporters ta buga wani labari mai take “Ku buge da Gura idan kun gansu” wanda a
yarda suka baiyana cewa “Attorney General” na Katsina Elmarzuk ya furta a yayin
da Gwamna Aminu Masari ya gaiyatu ‘yan Social Media buda baki Azumi a gidan gwamnati.
To Nidai a matsayina na shugaban Cliqq Magazine Nayi Allah wadarai da
Hotun (picture) da Katsina reporters tayi amfani wajen buga labarin ta ba tare
da daukar izinin (permission) mu ba.
Sannan kuma na hallarci wannan taro
da akayi da ‘yan Social Media wanda Alh Usman Ventures yayi jagora, Usman
Ventures yayi bayani matukar bayani wanda yayi kira ga Gwamna Masari da kamanta
adalchi a mulkin sa, Sannan kuma ya kara kira ga ‘yan Social Media da suji
tsoron Allah akan irin maganganu masu muni ko korafi mara amfani.
Daga nan Shugaban Katsina State Social Media Organisation
Dahiru Mani yayi bayani mai kyau a inda yayi ma Gwamna Magana akan Albashin ‘yan
kananan hukomumi da kuma akwatin “suggestion Box” da gwamnati tasa a wurare da
kauyuka a Katsina.
Ana shi jawabin, Elmarzuk(Attorney
general” yayi Magana ne akan halaiyar gwamna Masari ga yadda yake da hakuri da
kauda ido ga masu mashi shin fuska, da zagi wanda basu mashi adalchi . Sannan
ya kuma yi Magana akan masu zagin matan gwamna, ko ayi amfani da hotunan su don
shin fuska wanda yace ba ruwan mabiya da “personal Life “na Gwamna Masari.
Sannan ya kara da cewa ba za su yadda
da irin hakan ba ga yadda ake zagin iyalen su wanda bai da kyau ko a musulunci.
Ya kare maganar shi da cewa idan kuma masu zagin iyalen su hakanan don iyayen
gidajensu suna sa su don aikata hakan, to za su fara daukan matakan Shari’a
akan masu yin haka.
Ana ci jawabin, Gwamna Masari yayi Magana
sosai akan masu zagin shi ko iyalen sa. Wanda ya baiyana yace sau dayawa ana
mashi “text message” na zage zage wanda yace idan mutum yayi nafarko, sai ya
kauda ido, idan yayi na biyu ya kuma kara har sau ukku, to yana da hurumin yasa
hukuma ta jama masu layi don kada su koma.
A karshe gaskiyan Magana shine babu
inda El-marzuk yace Ku bege da gora idan
kun gansu, wannan kage ne da kuma raunin kafofin labaran mu na zamani.
Muda aka kulle damu dakai aciki wajen taro kuma ni dakai ko yasan abun da akayi wajen sai kazo kana karya ta abunda kaji da kunne ka don baka tsoron Allah. i will reveal the videos ko dan na gasgata wannan statement inna ka.
ReplyDeletewe are disappointed in you. Ranar Sallah amma kafito kayi ma mutane karya. ance dai idan zaka fadi zance ka fadi zance na gaskiya
ReplyDelete