Banso na chigaba da magana ba a wannan bangare, amma
ya zama wajibi nayi fashin ɓaki akan kalaman Hon. Umar Tata.
Mafi akasarin maganar da Hon. Umar Tata yake faɗa
shine Masari yafi Yakubu Lado Danmarke, chanchanta, Shiyasa Tata barin PDP zuwa
APC. Ta zahirin gaskiya wannan magana ba ita bace sanadiyyar barin Hon. Umar
Tata daga PDP zuwa APC ba.
Ina so jama'a
su gane cewa wannan bashi bane karon farko na ficewar sa daga PDP ba zuwa wani
waje, idan mai karatu bai manta ba a kakar zaɓe ta 2015 bayan kammala zaben
fidda gwani na takarar gwamna, Allah cikin ikon shi bai bama Hon. Umar Tata
nasara ba sai gashi Hon. Umar Tata yabar Jam'iyyar ya PDP ya koma mai zakara
wato APGA. Wannan lokacin a zaton shi shi zai ci zaɓe Jam'iyyar sa ta APGA,
amma Allah Shi daya tashi nuna Mashi ishara sai Allah yasa yayi na Karshe a
cikin yan takarar gwamnan.
Duk da haka Hon. Umar Tata bai dauki kaddarar faɗuwa
zaɓe ba, saida yayi karar Shahararren kamfanin sadarwar nan wato MTN cewa su
bashi kudin da ya kashe na takarar da yayi bai samu nasara ba, Kotu ta kori
karar saboda karar bata da tushe bare Makama.
A karo na biyu Hon. Umar Tata ya dawo PDP daga
Tsohuwar Jam'iyyar sa ta APGA ya taho dauke da posters din shi da bilbord da
zummar zaiyi takarar gwamna, kasancewar PDP gidan kowa da kowa ne aka bashi dukkan gatan daya dace domin ganin
an kyautata Mashi, haka Akaita hakuri dashi, yau yace yabar PDP gobe yace ya
dawo jibi kuma yace yabar siyasa, haka dai Akaita hakuri da juriya dashi duk da
kasancewar sa ta dan takarar neman Tikitin takara bawai dan neman cigaban
al'umma ba.
Bayan tafiya tayi nisa, babu dan takarar da yayi nisa
wajen ci da zuci kamar yadda Hon. Umar Tata Yayi, domin har mukamai ya fara
rabawa, irin wanda zababben Gwamna ya kamata yayi bawai mai neman takara ba.
Anan zanso al'umma su sani cewa PDP bata zalunci Hon.
Umar Tata ba, kamar yadda naji yana faɗa har a gidan radiyo, ina son jama'a su
sani cewa Hon. Umar Tata kaf zamu iya lissafa abunda ya kashe ma PDP a matsayin
Gudummuwa.
Zanso Jama'a su gane cewa Hon. Umar Tata yabar PDP ne
saboda rashin daukar kaddarar da Allah ya aza mashi ta faɗuwa zaɓen fidda
gwani, duk da kasancewar shi ta wanda ya fitar da tsarin da kan shi, kuma ya
rubuta da kanshi ya kuma saka hannu da kanshi, amma da yake ba jama'a ne a
gaban shi ba, son zuciyar shi yake bata jama'a yake ba, bai damu da Chigaban
al'umma ba, son mulki ne ya rufe masa ido, Shiyasa yake neman mulki ido rufe.
Tun a watannin baya duk al'ummar jihar katsina suka
fahimci cewa Masari bai chanchanci yayi tazarce ba a kakar zaɓe ta 2019. Muna
da dukkan abunda zaya nuna cewa kai kanka ka karya ta kanka Da Kanka Hon. Umar
Tata ka tabbatar ma duniya da hakan, wanda muna da hujjoji da yawa akan haka.
Hon. Umar Tata kada ka dauka cewa dole sai an baka
takara ko sai an baka mulki, Hakan baya cikin tsarin islama, Hon. Umar Tata
naji yaran ka har sun fara cewa 2023 daga Masari sai Tata, a ganina ai kayi
gaggawa da yawa, ina baka shawara kayi hakuri mukai 2019 ɗin mana sannan sai ka
fara Yima kanka Kamfe mana.
Ina kara sanar dakai cewa dole dan siyasa ya rinka
daukar kaddara, yasan samu da rashi duk na Allah ne.
Yanzun kenan daka samu takara a Jam'iyyar PDP, hakan
ba zaisa kabar PDP ba kenan, amma daga faɗuwa Zaɓen Fidda Gwani harka chanza
Sheƙa zuwa APC, babu shakka harna fara tausaya maka akan abunda zai iya zuwa ya
dawo, nasan zakayi nadama akan komawar ka A APC.
Daga karshe ina kara baiwa Hon. Umar Tata shawara ya
kiyaye cin mutuncin masu mutunci, idan za ayi rubutu banda sharri, banda Ƙage,
banda cin zarafi, domin yin hakan bazai haifar masa da Ɗa mai ido ba, domin shi
yanzun ya zama dattijon social media mai tallata hajar Gwamna Masari, kamar
yadda nike matashi mai tallata hajar Distinguish. Senator Yakubu Danmarke.
Allah ya bamu nasara.
North-West
PDP Social Media.
Nuraddeen
Adam Kankara Tina
No comments:
Post a Comment