Mafi yawan al'umma suna mamakin yadda Hon. Umar Tata
tare da yan koral din sa ke cewa Gwamna Masari yafi Senator Yakubu Garba Lado
Danmarke chanchanta, wannan shine dalilin Komawar Hon. Umar Tata APC kunga
kenan ko anan sun nunawa jama'a cewa ba saboda cigaban al'umma suka koma APC
Ba, Sun koma ne saboda son zuciyar su.
Idan jama'a Zasuyi duba da matsayin da Gwamna Masari
ya rike kafin yayi Gwamna zaku ga cewa Senator Yakubu bai rike shi ba, tunda
yayi Kwamishinan ruwa daya rike har zuwa Majalisar tarayyar Abuja har ya zama
speaker idan kaje Kafur ba zaka iske mutum Ukku wanda Gwamna Masari ya samar ma
aiki ba, Kaga Kenan idan har mutum zai rike muƙami na Ukku a Nigeria ya gaza
samarwa dangin sa aiki ai kaga baka hada su da wani mutum mai daraja ba
kwatankwacin Senator Yakubu Danmarke ba.
Babu wani aiki da DG Tata zai nuna a Masari Ward wanda
akayi lokacin da masari yake na Ukku a Kasar Nan.
An zabi Masari a matsayin dan majalisa mai wakiltar
Malumfashi/Kafur, haka aka gama Wakilcin majalisar tsawon shekaru 4 Babu ko
tsarabar Abuja ga al'ummar wannan yanki.
Haka kuma Gwamna Masari ya samu sa'ar yin tazarcen
kuma cikin ikon Allah aka zaɓe shi Speaker na Nigeria, amma a hakan al'ummar
yankin Malumfashi/Kafur kai harma da jihar katsina suna ɗoki suna murna nasu ya
samu Zaa kawo aikace-aikacen raya kasa da inganta rayuwar mazauna jihar nan
dama wajen jihar nan baki daya.
Amma mamadin mu samu cigaba sai muma samu akasin haka,
duk jama'a suka maida wukar su a bakin kube, domin basu ga wani aikin azo a
gani da yayi ba.
An yi speaker kala daban daban a Nigeria, tun daga
mulkin Demukuradiya har zuwa yanzun duk wanda ya rike speaker na kasa yana da
abun nunawa a jihar su, amma Gwamna Masari baya dashi, idan kuma yana dashi sai
a fili a faɗa mana shi ina jiran DG Tata dan tallar Masari ya nuna mana shi
koda a kafar sadarwar Facebook Ce.
Kowa Yasan Guguwa ta kawo majority ɗin masu mulkin
yanzun musamman Rt. Aminu Masari wanda DG Tata yake tallata hajar sa.
Cikin ikon Allah yanzun anyi ruwa Guguwa ta daddale,
babu sauran Guguwa a kakar zaɓe ta 2019 da yardar Allah, chanchanta Zaa duba ba
Sak ba.
Lokacin da Gwamna Masari yazo Katsina komai yana
tafiya daidai dukkan al'amurran jihar nan suna tafiya akan layi babu saɓa
number, amma yanzun a Kasar nan jihar katsina tana daga cikin koma baya a Kasar
Nan duk dan saboda irin rikon sakainar kashin da Gwamna Masari yayi mata.
Shekarun mu Ukku kenan muna gab da shiga ta Huɗu, amma
har yau babu abunda DG Tata zai iya nunawa na Masari wanda ya wuce rashin
tsaro, talauci da tada hankalin al'umma, sai kuma shegiyar abunda ta addabi
al'umma wato YUNWA, wanda kai kanka kasan ana yunwa shiyasa ma kaida kanka ka
Kirkiri Shirin "A KORI YUNWA" amma mamadin kaika kori yunwa, sai
gashi ita YUNWAR TA KORE KA, ɓuge da tallar dan takara akan million GOMA
10,00000.
Kamar yadda Hon. Umar Tata ko ince DG Tata ya faɗi a
wani taro da akayi wajen amsar Mustapha Radda, cewa al'umma su tashi tsaye
wajen karatun maganar karatun yayayen su da masari ya gaza biya masu kudin
waec/neco, Hakan ne ya tabbatar da gazawar APC tun a wannan lokacin har yanzun
gaskiya kara bayyana take a fili ta fuska daban daban, Hakan yana nuni da cewa
Insha Allahu Mune keda nasara kamar yadda na hannun damar ka Mustapha Radda ya
fadi cewa zaben 2019 PDP zata lashe shi, Dukkan Alamu sun tabbata na faɗuwar
zaben APC.
kullum babu wani Aiki daya wuce tura al'umma gidan
radiyo da telebishin da jaridu, domin a kare alkawarin da akayi aka kasa
cikawa.
Kowa Yasan cewa wannan gwamnatin babu abunda ta Chanza
sai maida na cikin inuwa a rana, maida na haske zuwa duhu, yuwan zuwa koshi da
dai sauran su.
A 2015 babu yadda engr. Musa Nashuni saida yace ma
al'umma cewa kada su jama'a su Kuskura su Chanza ilimi da ake ba yaran su
kyauta ko kuma albashi da ake biya akan lokaci. Bayan an Zaɓi gwamnatin APC
kuma engr. Musa Nashuni yace daman saida na faɗi maku cewa kada ku Chanza
ayyukan Alkhairin da Gwamna Shema yayi, amma saboda an rude ku da rokon baka
kuka chanxa, to gashi magana ta ta tabbata inji engr Musa Nashuni.
Daga karshe ina son DG Umar Tata ya sani jihar katsina
bata bukatar Gwamna Masari kuma da yardar Allah zamu amshi jihar nan a 2019.
Allah ya bamu ikon Korar Yunwa a kakar Zabe ta 2019
kamar yadda Hon. Umar Tata yake fata a baya kafin ya chanza ra'ayin sa akan
kudin tada koma ɗa da babban Attajiri ya bashi.
Nagode. Nuraddeen
Adam Kankara Chairman
SMO.
No comments:
Post a Comment