Alamu na nuna cewa Umar Abdullahi Tsauri zai
koma jam’iyar APC a jihar Katsina bisa rashin zama dan takarar kujerar gwamnan
jihar Katsina.
A yau jam’iyar PDP reshen jihar Katsina ta saida
Senator Yakubu Lado Danmarke a matsayin dan takarar ta na kujerar gwamna bayan
yar gajeruwar zabe daya gudana.
A binciken Cliqq Magazine Hausa ta
gano cewa akwai yan takara irin su Ahmed Aminu Yar’adua da suka ki amincewa da
salon da aka bi wajen yin zaben.
Amma magoya bayan Umar TATA tuni suka fara
ficewa daga jam’iyar PDP da yin Allah wadarai da rashin yin adalci ga yadda
shuwagabannin jam’iyar su kayi.
Daga cikin yaran TATA da suka fita akwai Abdul
Danja wanda shine mai taimaka mashi wajen sarrafa hanyoyin sadarwa na zamani.
Abdul ya baiyana ma Cliqq Magazine Hausa cewa
lallai shi ya fita daga PDP kuma yana fatan ubangidan sa Umar TATA ma zai fice
daga PDP.
Fitowar Senator Yakubu Lado a matsayin dan
takara ba abun mamaki bane ganin yadda aka dade ana rade radin cewa tsohon
gwamnan Katsina Ibrahim Shema ya hakikance akan dole sai Yakubu Lado.
Wata majiya mai karfi ta shaidama ma wakilin mu
cewa, a zaman da yan’takarar suka yi a satin da ya gabata, sun amince akan azo
ayi zaben fidda gwani da sharudda akan cewa baza ayi amfani da kudi ba musamman
ma wajen sayen daligat, amma wasu nazargin Yakubu lado da amfani da kudi ta
bayen fage.
Amma yanzu alamu na nuna cewa Umar Tata zai koma APC ganin irin rashin adalci da PDP tayi, amma wata majiyar daga gidan TATA sun baiyana ma wakilin mu cewa zasu dan saurara har zuwa sati daya kafin su fitar da sanarwar jam'iyar da zasu koma.
Tabbas PDP a Jihar Katsina ta tsunci kanta cikin
wani hali mai wuyan sha’ani musamman ma yadda talakan Katsina yake tsammani
zasu kamanta adalshi, tambaya anan shine, mene ne mafita ga irinsu Umar TATA da
sauran yan takarar?
No comments:
Post a Comment