Wanna ya biyu baya ne bisa labaru da
ke yawo a kafafan yada labaru na zamani akan cewa Bilyaminu Rimi ne sabon
shugaban jam’iyar APC.
Mujallar Cliqq Magazine Hausa ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki dake jam’iyar wanda
suka karyata labarin wanda ya kuma samu asali ne daga ‘yan adawa don batanci.
Saboda haka suna
kira ga al’ummar jihar Katsina da su guji yada jita-jita mara tushe don haddasa
husuma ga mutanen jihar Katsina.
A kwanakin baya, jam’iyar adawa PDP
ta jihar Katsina tayi Babban rashi bisa yadda wadansu jiga-jigan PDP suka kuma
zuwa jam’iya mai ci watau APC.
Daga cikin wadan da suka yi mubaya’a
zuwa APC sun hada da tsohon kakakin majilissar jihar Katsina ya dawu APC daga
Daura zone, Alh Musa Adamu (Funtua zone) da kuma Bilyaminu Rimi daga Katsina ta
tsakiya.
No comments:
Post a Comment