Wednesday, 21 June 2017

Masoyan Tata Ne Asalin Mayakanda Suke Haska PDP A Social Media Organization-Abdul Danja

Abdul Danja
Umar Tata shine kadai Wanda duk da karfin PDP a Katsina bayan ta fadi zabe saida yadawo ya motsa duk da dinbin mutane Wanda PDP ta daukaka a Katsina tun daga 1999 har zuwa yau amman sukai shiru duk da amfanin da PDP tayi masu suka manta ta suka barta a wajen majigiri shi daya da exco nashi saida tata yadawo cikin ta da duka masoyan shi da jama'ar da talakawan  shi sannan PDP ta motsa. A halin da muke ciki a yanzu duba da yanayin da muka tsinci kan mu babu Wanda ya raya PDP daga lokacin da ta fadi zabe zuwa yanzu illa tata da Majigiri.
Abun dubawa a nan shi ne mutanen nan da suka guji PDP babu abinda PDP bata yi masu ba,PDP tayi masu zani da Riga da wando da hula  amma abun takaici shi ne sun kyale PDP a lokacin da PDP ta fi bukatar su. Bayan anfadi zaben 2015 meyasa sukayi  shiru? Mi PDP taima Tata? Shin tayi mashi kamar yadda tayi masu? Idan ka duba tarihin siyasa Katsina da kuma PDP zakaga su wa'ancan jiga jigan da PDP tayi ma komai zakaga bashi mutanen Katsina suke binsu da PDP kanta amma tata shike bin PDP bashi domin yayita wahala da ita da mutane da suke cikin ta saboda ya daga darajatar ta ganin yanda party bai samu karbuwa ba a idon al'umma. Yayi kokarin nuna ma duniya cewa PDP ita ce jam'iyya mai adalci da sanin ya kamata a katsina,jam'iyyar dake share ma talaka kukan shi ta kuma yimai adalci. Zaman tata cikin PDP ya nuna ma duniya cewa a katsina PDP jam'iyya ce mai adalci tunda akwai irin su tata a cikin ta.

Social media ganin yadda PDP take tashe a jahar Katsina a duka arewacin Nigeria a yau babu inda ake maganar PDP kamar katsina saboda yawan magoya bayan tata yadda suke aiki a media babu dare babu rana dan kawo mafita a jihar Katsina. Kamfen din da suke ma tata ya shafi tallata PDP ita kanta shiyisa nace 'yan social media na gidan tata sun taimaka wajen tallata PDP da kuma daukaka ta. Don haka ashe kuwa sune asalin mayakan da suke tallata PDP a duniya da kuma  social media baki daya. Ganin yadda suke wannan namijin kokarin shiyasa kullum ake kawo masu hari a koda yaushe,ba'a dauki wani lokaci mai tsawo ba da APC dawasu yantakara a Jamiyyah  sukaita zawarcin  na   sayen  ra'ayin shugabanci dakuma members  na umar tata social media  Wanda daga karshe masoya tatan suka ki amincewa domin amana dakuma yadda  sabida  siyasa suke ta akida,rikon amana da kuma juriya saboda haka babu wani mutum ko kudi da zasu iya siyen ra'ayin su.

Dawowar siyasar tata a 2019 za'a  gina ta ne bisa akida,amana,juriya domin neman ticket da kuma tunkarar APC kai tsaye. A APC duk wanda ya fita ko kuma aka siye shi dama chan ba dan siyasa bane ko kuma baida akida irin ta gidan mu,mutane kullum dafifi suke yi domin shigowa da jarinsu da jama'ar su domin taimakawa wajen samun nasarar takarar Umar Tata akan yakin Neman zaben 2019. Akida ta siyasar gidan Tata ita ke tsayar da mutane gidan bawai a sawo mutum da kudi ba. Wa'annan dasu mutane masu akida dasu ne zamu shiga gidan gwamnati 2019 da yardar Allah.

Umar Tata da magoya bayan shi suna ma jam'iyya biyayya a ko wane mataki da kuma jinjina ga hon Salisu majigiri ga me da kokarin shi na yin adalci a PDP baki daya
Saidai guguwar adawa yanzu a zuciyar talakawan Katsina a wannan karnin ta karkata ne bisa son tata kawai domin samama PDP nasara da amsar mulki a hannun APC.

Babu wani laifi da wani dan siyasar gidan Tata yayi domin kauna ce tsantsa da kuma nuna dan takarar su da suke yi. Mu masu biyayya ne ga kowa Umar Tata yana da Hali mai kyau da kuma abin tallatawa shiyisa kullum masoya suke dafifi akan tafiyar shi saboda suna kyautata zaton shi kadai ne mafita a zabe mai zuwa. Ina fatan hon Salisu majigiri zai tsaya yayi adalci kamar yanda ya fada a baya saboda adalcin ne kadai zai ceci katsina a 2019.

Sign Comr Abdulrahaman Haruna Danja
State Chairman Umar Tata Social Media

 

No comments:

Post a Comment