Wednesday, 7 February 2018

Siyasa | Ana Shirin Yi Wa Shugaban APC Reshen Katsina Kora Da Hali

Rahotannin da suke yawo a yanzu musamman a kafar sadarwa ta soshiyal mildiya shi ne ana kokarin yi wa shugaban riko na Jam’iyyar APC Malam Shitu S. Shitu kora da hali wanda masu iya magana suka ce ya fi kora da kara. Ya zuwa yanzu dai hotanan tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Honarabil Bilyaminu Rimi ake ta yadawa ana yi masa murnar samun shugabancin jam’iyyar APC na riko a jihar Katsina.
Sai dai ba tare da bata lokaci ba, wasu daga cikin magoya bayan shugaban riko mai ci yanzu, suka fara maida martani da cewa wannan labarin kanzon kurege ne babu gaskiya acikinsa. Haka kuma sun alakanta wannan labari da cewa ‘yan adawa suke kunno wannan wutar saboda jin haushin ficewar Honarabul Bilyaminu Rimi daga jam’iyyar PDP a watan da ya gabata.
Da ma dai ana ta sokar shugabancin jam’iyyar APC daga ciki da wajanta saboda abinda wasu suka bayyana cewa jam’iyyar babu shugabanci, mutun daya rak ke wasa da akn macijin, shi yasan halin da take ciki, ya kuma hana kowa matsawa kusa, hatta su kansu ‘yan jam’iyyar sun koma saniyar ware Kazalika an yi zargin cewa ko dai masaniyar gwamna Aminu Bello Masari wannan al’amari ke tafiya a haka kuma ana yi masa baluluba, inda da yawan lokuta jam’iyyar ta kan yi burus da duk wani kalubale na ‘yan adawa, su kan kasa maida martani, sai dai su zuba na mujiya ana yi wa jam’iyyar cin kashi, ta hanyar kafar sadarawa ta zaman.
Yanzu haka babban ofishin jam’iyyar APC da ke Katsina ana yi masa kirari da ‘’gidan mantuwa’’ kuma ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na halsa ne suke fadin haka sakamakon yadda kowa ya kama gabansa ya kyalesu suna zaman jiran tsammani, kuma idan ka ga wani a wajan sai da babban dalili. Wabi abun ya kara fusata magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Katsina shi ne rashin yin aikin da ya rataya akan jam’iyyar APC a jihar Katsina ya samar da bullar kungiyoyi da suka nuna sha’awarsu ta taimawa gwamna Masari a zabe mai zuwa inda yanzu ake da kungiyoyi da suka kai dubu daya.
To amma kwatsam sai shugaban riko na jam’iyyar APC Malam Shitu Maslaha ya ce a matsayinsu na jam’iyyar ba su san kowace kungiya ba, sai wata kwara daya mai suna Masariya da wani tsohon da jam’iyyar PDM ya kirkira domin cimma manufar siyasa. Wadannan na daga cikin dalillan da wasu ke ganin an kyauta in dai har aka baiwa Honorabul Bilyaminu Rimi shubancin jam’iyyar, domin ko ba komi zabe ke tafe kuma ana bukatar wadanda za su kai jam’iyyar ta APC tudun mun tsira a zabe mai zuwa.
Wannan ma ya kara tabbatar da zargin da wasu ke yi na cewar ko dai gwamna Aminu Bello ya ga ji yawan koke akan shugabancin wannan jam’iyya ko kuma ana son yi wa shugaban riko na APC kora da hali domin ya je ya fuskanci sana’arsa tunda daman ba zaman kashe wando yake ba. A lokacin da na tuntubi wani na kusa da Honorabu Bilya Rimi domin jin ina wannan magana ta ta so, cewa gaskiya suna sa ran haka amma dai har yanzu bata tabbata ba, ‘’ sannan ya kara da cewa akwai maganar amma dai yanzu ba a kai ga bada sanarwa ba, kuma muna da kyakkyawar fatan cewa shi za a ba rikon jam’iyyar’’ in ji shi.
A bangaran shugabn riko na jam’iyyar APC a jihar Katsina Malam Shitu S. Shitu cewa ya yi, yanzu da nake maganar nan da ke gamu tare da sauran shuwagabannin jam’iyyar muna tattauna yadda za mu kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau litinin kuma nine nake shugabantar tafiyar, domin nuna goyan bayanmu da sauran batutuwa’’ in ji shi.
Sannan maganar cewa an baiwa Biliya Rimi shugabanci jam’iyya, shi kanshi Biliyan din ya kirani ya kuma da mu so sai da jin wannan magana amma dai ya fada masu ko su wanene suka shirya wannan cin fuskar da yarfan siyasar. Acewarsa Biliyan sai ranar 25 ga wannan watan sannan jam’iyyar zata amshe shi kamar yadda ka’ida ta nuna sannan zai zama cikakken dan jam’iyyar, wanda daga nan ne zai iya shiga neman takarar shugabancin jam’iyyar tunda anan gaba kadan za a yi zaban sabbin shuwagabanni. Alhaji Shitu S. Shitu ya ce, idan har aka yi la’akari da abinda jama’a ke fada an sabawa kudin tsarin mulkin jam’iyya kuma idan ba a manta ba, gwamna shi ne shugaban jam’iyya a jaha, wannan ya nuna cewa wancan magana ta Biliya akwai tasgaro a cikinta.
Asalin Labari : Leadership Hausa


No comments:

Post a Comment