A yau Alhamis a unguwar Daki Tara aka tsinci wani
dan jariri sabon haihuwa a cikin wata bula da ke kusa da bakin titi a cikin
kwali kunshe a kwance.
Cliqqmagazinehausa.blogspot.com ta isa wajen
inda ta gane wa idon ta wannan abun kyama da ban mamaki. Yara Almajirai, Yan
mata manya da yara duka sun zagaye wannan yaro ana ta kallon shi da yin wadarai
ga duk wanda ya aikata wannan abu.
Lafiyar yaron shine ba tabbas, shin yana da rai
shima ba tabbas domin ga yadda aka samu jaririn ana tunani an shire masa rai
wajen zubar da cikin.
Wannan ya faru a lokacin azumi, lokacin da ake su
jama’a su da ge wajen yin bauta da neman gafara amma duk da haka an samu wasu
fitsararru da suka aikata wannan mummunan aiki.
Da wakilin mu ya tambayi mutanen unguwar, sun
shaida mashi da cewa su sun tashi safiyar yau suka ga wannan abu batanci.
Allah ubangiji ya fallasa asirin wadan da suka
aikata wannan ta’asa.
No comments:
Post a Comment