Monday, 29 January 2018

Siyasa | Abubakar Tsanni yayi alkawarin N1miliyan daya ga duk karamar hukumar da zabi Masari


Shugaban kungiyar Masariyya ta jahar Katsina yayi alkwarin naira miliyan daya ga duk karamar hukumar da ta ba Gwamna Masari kuriu dari da hamsi a zabe mai zuwa.

Shugaban kungiyar Masariyya, Abubakar Tsanni yayi wannan bayani a lokacin da ya kaddamar da sabon offishin Masariyya dake Kusada da kuma shuwagannin Masariya a garin Ingawa da Kusada.

A cikin bayanin shi, yayi baiyana dalillai da yasa aka kafa wannan kungiya domin samar ma mai girma Gwamna Aminu Bello Masari kuri’u miliyan guda a zabe mai zuwa.
Abubakar Tsanni
Shugaban kungiyar Masariyya

Shugaban yayi kira ga magoya bayan da su kauraci siyasar batanci domin su mai da hankali wajen cinma nasarorin su.

Abubakar Tsanni ya kara da cewa babu wani gwamna da aka dabayi a jihar Katsina wanda yake da abubuwan na Alheri da yayi wa talakawan jihar Katsina domin shi mutum ne mai rikon gaskiya da amana wajen tattalin dukiyar al’umma.

Shugaban Masariyya ya baiyana godiyar shi ga commissioner na ma’aikatar albarkatun cikin kasa Hon. Mustapha Kanti Bello wajen gudmmuwar da yake ba kungiyar. Haka zalika ya jinjina ma shugaban kakakin majilissar jihar Katsina RT. Hon Yahaya Kusada wajen jajir cewa game da tallafin offishi da ya ba kungiya a garin Kusada.

Daga farko shugaban tafiyar da harkokin kungiyar Masariyya ta jihar Katsina, Alh Yau yayi kira ga sabbin  shuwagannin Masariyya ta karamar hukumar Ingawa dasu yi aiki tukuru domin ganin an cimma nasara.
Alh Sule Aruwa
Shugaban jam'iyar APC Karamar hukumar Ingawa
Alh Yau ya kuma kara da cewa talakawa sun gamsu da salon mulkin Gwamna Masari wajen dawo da martabar jihar katsina ta fannoni daban-daban.
A kuma na shi jawabin, Shugaban jam’iyar APC na karamar hukumar Ingawa Alh Sule Aruwa yace mutanen Ingawa basu da wani dan-takara  wanda ya wuce shugaba Buhari da Gwamna Masari a zabe mai zuwa.

Shugaban ya nuna jin dadin shi akan irin jajir cewar kungiyar Masariyya wanda ya sha alwashin taimaka ma kungiyar Masariyya dari bisa dari.

Sabon offishi Masariyya dake Kusada
Kadan daga cikin wadan da suka yi Magana sun hada da shugabar mata ta kungiyar Masariyya Hajia Amina Mani da kuma Shugaban tafiyar da harkokin kungiyar Masariyya na karamar hukumar Ingawa.


Hajia Amina Mani tare da Abubakar Tsanni
Shugaban Kungiyar Masariyya ya samu rakiyar dakarun masu yada kafar labaru na zamani irinsu Hamisu Hara, Abubakar Shafi’I Alolo da Suraju Yandaki

 

No comments:

Post a Comment