Gwamnatin jihar Katsina na ci-gaba da mayarwa iyayen yara kudaden jarabawa da suka biya na daliban da suka fadi jarabawar mock (Qualifying exam) amma suka ci a-kalla kiredit 5 da ya hada da turanci da lissafi.
DG Katsina Media and Publicity, Malam
Ibrahim Muazzam ya sanar da haka ga manema labarai a Katsina.
Malam Ibrahim Muazzam yace wannan cikon alkawari ne da Gwamna Aminu Bello Masari ya dauka, cewa "duk wanda ya biya wa dan sa kudin jarabawa amma dan nasa yaci a-kalla kiredit biyar (5 credit and above) da ya hada da turanci da lissafi, to gwamnati zata mayar masa kudin sa".
Malam Ibrahim Muazzam yace wannan cikon alkawari ne da Gwamna Aminu Bello Masari ya dauka, cewa "duk wanda ya biya wa dan sa kudin jarabawa amma dan nasa yaci a-kalla kiredit biyar (5 credit and above) da ya hada da turanci da lissafi, to gwamnati zata mayar masa kudin sa".
Malam Ibrahim Muazzam yace wannan ya
nuna dattakon Gwamna Aminu Bello Masari da kuma damuwarsa ga ci-gaba bangaren
ilimi.
Yace yazuwa yanzu, gwamnatin jihar ta
kashe sama da Naira miliyon tamanin (N80m) wajen biyan kudin jarabawar WAEC da
NECO ga iyayen yara.
Ya lura cewa tun daga lokacin da aka
kirkiro wannan kuduri, an samu ci-gaba wajen yawan daliban jihar dake cin
jarabawar WAEC din da NECO.
DG Media din ya bayyana cewa yawan
yaran dake cin jarabawar WAEC ya karu daga kashi 6 cikin dari (6%) zuwa kashi
55% cikin dari, alhali yawan daliban dake cin jarabawar NECO a jihar ya karu
daga kashi 7% cikin dari zuwa kashi 72% cikin dari.
Yace daama nufin gwamnatin jihar shine
don a zaburar da daliban jihar su kara mayar da hankali kan karatunsu.
Don haka Malam Ibrahim Muazzam ya
bukaci iyaye su kara mayar da hankali kan karatun 'ya'yansu domin su zama
hazikai a makaranta.
Asali
DG Katsina Media and Publicity,
Ibrahim Muazzam Abdullahi
DG Katsina Media and Publicity,
Ibrahim Muazzam Abdullahi
No comments:
Post a Comment