Majalisar Zartarwa ta jihar Katsina ta amince da daftarin kasafin kudin jihar na shekarar dubu biyu da sha takwas, 2018.
Mai bai wa Gwamna Aminu Bello Masari shawara kan kasafin kudi, Malam Abdullahi Imam ya sanar da haka jim kadan bayan ganawar majalisar ta mako-mako.
Malam Abdullahi Imam yace Gwamna Aminu Bello Masari ya jagoranci zaman majalisar a gidan gwamnati dake Katsina.
Yace gwamnan zai gabatar da daftarin kasafin kudin a zauren majalisar ranar litini mai zuwa.
No comments:
Post a Comment