Wednesday, 8 November 2017

Kungiyar Likitoci Ta Kasa Ta Bai Wa Gwamna Masari Lambar Yabo Na Aiyukan Inganta Bangaren Kiwon Lafiya


Kungiyar likitoci ta kasa, NMA, ta bai wa Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina lambar yabo bisa hobbasan da yake yi domin inganta bangaren kiwon lafiya a jihar.

Kungiyar ta ba gwamnan lambar yabon ne yayin da tawagar shuwagabannin kungiyar suka ziyarci gwamnan a gidan gwamnati dake Katsina.
Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Dr. Kingsley Ekweremadu, ya yaba wa gwamnan bisa aikin gyaran asibitoci da gwamnatinsa ke aiwatarwa, musamman manyan asibitocin dake Katsina da Funtua da Daura.

Ya kuma jinjina wa gwamnan bisa kudurinsa na gina asibitin koyarwa, wanda za a hada da sashen koyar da aikin likita da ake da niyyar ginawa a jami'ar tunawa da Umaru Musa Yaradua dake Katsina.

Dr. Ekweremadu ya kuma lura cewa duk da matsatsi na karancin kudaden shiga, gwamnatin jihar Katsina har yau bata gaza biyan hakkokin likitoci da malaman asibiti da sauran ma'aikatan bangaren kiwon lafiya ba.

Da yake mai da jawabi jim kadan bayan ya amshi lambar yabon, Gwamna Aminu Masari ya bayar da tabbaci cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar aiwatar da wasu muhimman tsare-tsare na inganta sashen kiwon lafiya a jihar.

Ya sha alwashin cewa nan da shekaru hudu babu dan jihar da zai je neman kiwon lafiya a wajen jihar, duba da irin na'urori na zamani da wadatattun likitoci da gwamnati ke shirin samarwa a jihar.

Yayin da shugaban kungiyar likitoci reshen jihar Katsina, Dr. Muhammad Usman ke gabatar da jawabin godiya, ya bayyana lambar yabon da aka bai wa gwamnan a matsayin karamci wanda ya dace.

No comments:

Post a Comment