Jami’ar Al-Qalam da ke Katsina na sanar da wadanda suka nemi shiga Jami’ar, cewa anfara tantance takardun su na Zangon karatun shekarar Alif Dubu Biyu da Goma Sha Bakwai zuwa Goma Sha Takwas (2017/2018).
Saboda haka ana
shawartarsu da su gaggauta shiga adereshin yanar gizon jami’ar watau a www.auk.edu.ng domin samun Karin bayanin ranar
da zasu zo da takardunsu.
Har ilayau,
Makarantar Gaba da Digri na Farko da ke Jami’ar watau (School of Postgraduate
Studies) na sanar da jama’a cewa ta fara saida Form na daukan dalibai na Zangon
karatun shekara Alif Dubu Biyu da Goma Sha Bakwai zuwa Goma Sha Takwas
(2017/2018).
Ana iya samun Karin bayani
a cikin shafin yanar gizo na Jami’ar a forms.auk.edu.ng
Duk biyan kudaden za
ayisune ta yanar gizo da taimakon katin banki na ATM watau MasterCard, Visa ko kuma Valve
Card.
Hukumar Jami’ar Al-Qalam, Katsina
(Jami’ar Musulunci ta farko a Nigeria)
No comments:
Post a Comment