Wednesday, 15 November 2017

Jiga-Jigan Da Suka Assasa Masari Restoration Awareness Forum Sun yi Watsi Da Kungiyar.


Jiga-Jigan da suka assasa kungiyar Masu wayar da kan jama’a akan Maradun gwamnatin Masari watau ‘Masari Restoration Awareness Forum’ sun fita daga cikin kungiyar bisa dalillai wanda har yanzu basu baiyana ba.

Cikin wadanda suka fita daga cikin kungiyar akawai shahararen dan social media Shafi Alolo da kuma Surajo Yandaki.

Cliqq Magazine Hausa ta samu labarin daga shafin su na kafar zamani watau Facebook in da suka ce sun aje mukamansu gaba daya.

Karanta cikakken bayanin su a kasa

"YAU 14/11/2017 NA AJE MUKAMINA NA FINANCIAL SECRETARY MASARI RESTORATION AWARENESS FORUM"

Salaam, Ni Abubakar Shafi'i Alolo Ina Shedama Duniya cewa na Aje Muka...mina da nike riko a matsayin wucin Gadi na FINANCIAL SECRETARY a Kungiyar Masari Restoration Awareness forum. Ina kuma tabbatarma da Dukkan Membobin Wannan Kungiya zamuci gaba da zumunci kamar yanda aka Saba.

Daga Karshe Kuma inama Chairman dinta na Riko Alh Sabo Musa Hassan fatan alkhairi. Kuma muna nan a tafiyar Maigirma Gwamna 2019 ya maimaita Insha Allahu.
Kuma muna masu Biyayya ga Shugabancin Jama'iyya da dukkan wani shugaba dake cikin Jama'iyyar Apc. Bislm

Abubakar Shafi'i Alolo
Masariyya Alheri ce
14/11/2019

 

No comments:

Post a Comment