A wata jita jitar dake yawo a social media da jaridu na yanar gizo cewa kansilolin pdp na jahar katsina guda 330 sun koma apc.
To wannan
labarin ba gaskia bane, domin ko jiya mafi yawan su sun halarci taron national
delegate da aka gudanar a kowa ce karamar hukuma dake jahar katsina, Haka kuma
a ranar 20th ga watan nuwanba 2017 sun gudanar da zama a babbar sakatariyar pdp
ta jahar katsina karkashin jagorancin uwar jam'iyyar pdp ta jahar katsina.
Inda suka
zabi sababbin shuwagabannin kungiyar karkashin jagorancin hon. Abubakar ibrahim
yantaba, daga mazabar wakilin Kudu 1 da ke karamar hukumar katsina.
Zaben ya
samu halartar kansiloli guda dari ukku da goma Sha daya 311 cikin kansiloli
guda dari ukku da sitin da daya 361
Jim kadan
kuma suka yi hira da yan jaridu na kafofin ya ɗa labarai daban daban wanda an
sanya shirin a gidan rediyon vision fm katsina.
Hon. danlami
kurfi ya gaisa da wasu daga cikin kansilolin pdp na dutsinma da kurfi wanda aka
dauki hoton su, su tara aka tura a facebook wanda daga baya kansilolin dutsinma
da kurfi suka karyata abin.
Ga mai
bukatar jin muryar su da ganin hotunan su a gurin taro to saiya neme mu a
shafukan mu domin gane ma idon shi.
Daga karshe
muna son yin amfani da wannan dama domin karyata abinda ake ya dawa na jita
jita domin biyan wata bukata can daban duk da wannan ba bakon abu bane a apc
aikin ta ke nan karya da yada jita jita wanda daga karshe ake jin kunya idan
alumma suka gane hakan karya ce, kuma wannan na nuna gazawar apc karar domin
daace basu gaza ba to da tuni alumma sun bisu koda baa bada ko naira ba.
Hon.
Nuraddeen adam kankara tina
Chairman
Katsina State PDP Social Media.
Chairman
Katsina State PDP Social Media.
No comments:
Post a Comment