
- Wata matashiya ta bayyana dalilin da yasa mata ke shiga harkar shaye-shaye a jihar Katsina
- A cewarta takaicin maza ke haddasa hakan
- Saulawa tace idan ba’a shawo kan wannan matsala cikin gaggawa ba, za’a samu karin tabarbarewa tarbiya
Wata matashiya a jihar Katsina da aka ambata da suna Khadija Saulawa ta bayyana yadda takaicin maza ke sanya matan jihar shaye-shaye.
Saulawa, ma'assashiyar wata kungiya mai zaman kanta ‘Queen Dijah Women and Children Awareness Initiative’ tace kudirin ta shine ta wayar da kawunan mata akan illolin dake tattare da wannan harka.
A wata zantawa da tayi da jaridar Vanguard, Saulawa tace idan ba’a shawo kan wannan matsala cikin gaggawa ba, za’a samu karin tabarbarewa tarbiya a nan gaba.
Saboda a cewar ta “Idan kullum uwa na cikin maye wa zai kula da yara?”

Ta ce yawanci mata na shiga harkar shaye-shaye ne da zaran an fada masu cewa zai kawar masu da bakin cikin da mazajen su suka sanya su a ciki.
Ta ce da sun dandana suka ji dadi, shikenan ba za su iya dainawa ba.
Saulawa ta kuma ce kungiyar ta ta za ta mayar da hankali a bangaren fyaden kananan yara, wanda ta ce shi ma ya zama ruwan dare a Katsina da samar da tsaftataccen ruwan sha.
Ku same mu a www.facebook.com/Cliqq.Magazine
Ko Whatsapp @ 07032183026
No comments:
Post a Comment