
- Shahararriyar yar siyasar nan da ta fito daga karamar hukumar Funtua a jihar Katsina, Hajiya Zainab Ghana ta bayyana cewa akwai yiyuwar ta tsaya takarar majalisar garin na Funtua a zabe mai zuwa.
- Zainab Ghana wacce ta bada gagarumar gudunmowa wajen kafa
jam’iyyar APC a Katsina dama kasa baki daya ta ce Al’umma na yawan kiranka akan
ta tsaya takara.
- A cewar Zainab Ghana, Kiraye Kirayen Al’ummar karamar
hukumar Funtua na nuni da cewa Mazan da suke wakiltarsu sun kaa biya masu
bukatunsu, don haka akwai bukatar baiwa mata dama don suma su taka irin tasu
rawar.
A zantawar tad a wakilin ClIQQ Magazine ta wayar salula, Hajiya Zainab Ghana ta bayyana wa Sani Hamza Funtua dalilan da ka iya tilasta mata
fitowa takarar majalisa don wakiltar Funtua a majalisar dokoki ta jihar a zabe
mai zuwa.
“Da farko ban taba kawo
ma raina cewa zan tsaya takara ba, har zuwa yanzu da nike Magana dakai ban
yanke hukunci akan kiraye kirayen mutane na in fito takara ba, amma ba wai
hakan na nufin b azan fito takarar ba.
“A kowace
rana idan nah au kafafen sada zumunta na zamani musamman ma irinsu Facebook da
Whatsapp, nakan ci karo da sakunan mutane da yawa na cewa in zo in wakilce su a
matakin jiha. Hakan ke sa ni tunanin cewa watakila saboda mazan sun kasa cika
masu alkawuran da suka daukar masu ne yasa suke so na fito takara”

Hajiya Zainab Ghana dai ta dade tana gwagwarmaya don ganin cewa karamar hukumar Funtua taci gaba, kamar yadda tace:
“Ni yar siyasa ce, bani da wani buri day a wuce inga karamar hukumar Funtua taci gaba, musamman ma idan muka duba irin matsalolin da garin ke fuskanta.
“Har zuwa
yanzu, an maida mata shanun ware a dukkanin wasu sha’anoni na siyasa ko
tallafi, kuma sune ake neman kuri’arsu idan zabe yazo, amma da zaran zabe ya
wuce, shi kenan an maida su ba a bakin komai ba. Ina da burin ganin cewa Mata
sun ci gajiyar romon demokaradiya, ina so inga cewa zaman banza a tsakanin
matasanmu ya kare.
“Matsalolin
da Funtua ke fuskanta sun hada da rashin ababen more rayuwa, rashiin aikinyi a
tsakanin matasa, rashin bada tallafi na karatu ko kuma koyar da al’umma sana’o’in
hannu, uwa uba maida matasa yan bangar siyasa.”
Hajiya Zainab, Ta bayyana cewa, idan har ta samu dama, zata tabbatar
da cewa Karamar Hukumar Funtua ta zamo zakaran gwajin dafi a kananan hukumomin
jihar Katsina.
Daga Karshe tayii kira ga dukkanin mutanen dake yi mata fatan
alkairi da kuma son ta fito takara dasuyi hakuri, idan hart a yanke shawara kan
hakan, babu abinda zai hanata fitowa.
“Ga wadanda ke kirana
ta waya, ko aika min da sako ta yanar gizo, ina godiya kuma ina kan tunani akan
wannan kira nasu, tabbas b azan zura idanu in kyale Funtua taci gaba da tafiya
cikin duhu ba, idan har na shirya, to zan sanar wa al’umma hukuncin dana yanke.”
Wannan dai shine kusan karo na farko tun kafa karamar hukumar
Funtua, inda al’umma ke neman mace ta tsaya takarar majalisa don wakiltarsu a
matakin jiha, wannan kuma na daya daga cikin nasarar demokaradiya na baiwa ko
wane jinsi dammar yin zabe ko tsaya takara don a zabe shi.


Daga Teburin Edita: Sani Hamza Funtua
Whatsapp Only @ 07032183026
No comments:
Post a Comment