Thursday, 28 September 2017

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, Na Neman Shugabancin Nigeria

Gwamnan jihar Ekiti a Najeriya Ayodele Fayose ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2019.

Fayose

Mista Fayose wanda dan jam'iyyar adawa ta PDP ne, yana yawan sukan manufofin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, mai mulki.

Jam'iyyar APC, wacce ta karbi shugabancin Najeriya kusan shekara biyu da su wuce, ba kasafai ake jin duriyar jam'iyyar adawa ta PDP ba wacce take fama da rikicin cikin gida.



Jam'iyyar PDP wancce tayi shekara 16 tana shugabancin Najeriya kafin ta sha kayi a hannun a APC a shekarar 2015.

Fayose ya fara zama gwamnan jihar Ekiti wadda yankin take kudu-maso-yammacin kasar ne a shekarar 2003, kafin ya sake zama gwamnan jihar a shekarar 2014.

Zuwa yanzu dai shi ne mutum na farko da ya bayyana aniyyarsa ta neman shugabancin kasar a hukumance

Domin Tallace Tallace 07032183026

No comments:

Post a Comment