Saturday, 23 September 2017

Nayi Farin Ciki Da Mutuwar Umar Yar’adua A cewar El-Rufa’i


A wani fefan murya da aka nada wanda jaridar Daily Nigerian ta samu  an jiyo gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, yana cewa yayi farin ciki da jin mutuwar tsohon shugaban kasa Umar Musa Yar’adua, saboda ya samu labarin cewa marigayin na shirin saka masa cutar kanjamau da kuma ciwon hanta da zarar ya dawo Najeriya a wancan lokaci. 

 Da yake ansa tambaya a wani yanayi dake nuna kamar hira yake ana yimasa tambaya yana bada amsa, El-Rufai yayi karin haske kan tambayar da aka yi masa akan mutuwar Yar’adua.

” yanzu game da tambayarka kan mutuwar Yar’adua, ina godewa Allah da yabarni a raye shi kuma Umar ya mutu saboda ya so ya kashe ni.”

“Kasan cewa akwai shirin da akayi na a saka min cutar HIV da kuma ciwon hanta a tare, ta hanyar allura da zarar na dawo Najeriya. 

“Wannan ne abinda naji, ban sani ba gaskiya ne ko kuma ba gaskiya bane, amma dai tunda ina raye shi kuma ya mutu ai dole na godewa Allah, duk da cewa duk abinda zai same ka mukaddari ne daga Allah, ” El-Rufa’i yace.
Source:http://bbchausawa.com/nayi-farin-ciki-da-mutuwar-umar-yaradua-a-cewar-el-rufai/

 

No comments:

Post a Comment