Tuesday, 26 September 2017

A SHIRYE MUKE MU YAKI RUNDUNAR SOJIN NIGERIA

 

- Dakarun  Yankin Biafra (BNG) sun bada tabbacin cewa a shirye suke don yakar rundunar sojin Nigeria.
- Wannan ya biyo bayan hukuncin da Rundunar Sojin Nigeria ta yanke na sanya Kungiyar masu fafutukar kafa yankin Biafra daga cikin Kungiyoyin ‘yan tada kayar baya.
- Dakarun Yanikin Biafra sun sha alwashin kare al’ummar dake zaune a Kudu maso Gabashin kasarnan daga dukkanin wasu hare-hare.

An ruwaito dai cewa dakarun na BNG sunyi kira ga dakarun sojin Nigeria inda suke shaida masu cewa a shirye suke su kare jama’arsu dake yankin Kudu maso Gabashin kasarnan daga dukkanin wasu hare-hare.

Haka zalika Kungiyar ta BNG ta kalubalanci hukuncin da rundunar sojin Nigeria ta yanke na sanya kungiyar IPOB a cikin jerin kungiyar yan tada kayar baya a cikin wata sanarwa data aikewa kafafen watsa labarai.

Dakarun Yankin Biafra, sun bayyana cewa ba za’a yaudaresu ba ta hanyar manna masu lambar ta’addanci, tare da jaddada cewa nab a da jimawa baza’a tabbatar da yankin Biafra.

Manjo Nkuma, wanda shine mai Magana da yawun kungiyar yace su ba kungiyar ‘yan ta’adda bane, tare da karawa da cewa Abin ayiwa gwamnatin Nigeria dariya ne dan kuwa wannan hukunci kamar tatsuniyar gizo da koki ce.

Sanarwar ta ce : “Kada gwamnatin Nigeria ta taba tunanin samun kariya don kuwa kungiyar ba zata taba mika wuya ba har sai idan rai yayi halinsa”

“Ba abin al’ajabi bane ga Dakarun Yankin Biafra cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hannun Dakarun Sojin Nigeria ya sanya kungiyar dake fafutukar kafa yankin Biafra daga cikin kungiyoyin ta’adda.

“Bari mu tunasar da kasar Nigeria cewa Kungiyar IPOB ba wai kungiya bace kawai, IPOB wata al’umma ce ta mutanen dake zaune a yankin Gabashin Nigeria, don haka, daukar IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda na nufin cewa duk wani dan yankin Biafra shima dan ta’adda ne.

“Hakika abin takaici ne da muka tsinki kawunan mu a cikin kasar da ake kallon mu a matsayin ‘yan ta’adda, haka zalika kasar da bamu da wani yanci neman shugabancin kai-da-kai.

“Mu Dakarun Yankin Biafra, munyi amanna da cewa sanyamu a cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda na nufin kawo karshen tunanin al’ummar dake zaune a yankin Biafra dake ta fafutukar ganin an kafa yankin cikin ruwan sanyi. Abin tambayar a nan shine; shin zamu tsaya mu zura masu idanuwa har su tabbatar da yankin namu a matsayin saniyar ware da kuma zaman mu a matsayin ‘yan ta’adda kamar yadda suka sanar?

“Yana da matukar muhimmanci mu sanar da cewa Dakarun Yankin Biafra BNG ta dade da kafuwa tsawon shekaru, sabanin yadda rundunar sojin Nigeria ke cewa ta kwana kwanan nan ce, kuma dakarun suna cin gashin kansu ne da nufin kare yankin gabashin kasar nan kamar yadda yake a cikin tsarin yanci na majalisar dinkin duniya na 2007.

“Kungiyar dake fafutukar kafa yankin Biafra, karkashin jagorancin Mazi Nmandi Kanu, it ace Uwar ko wace kungiya dake da alaka da yankin Biafra, don haka, duk wani dan yankin ya fada a cikin wannan kungiya.

“Dakarun Yankin Biafra BNG na zamankanta ne kuma bata da wata alaka da kungiyar IPOB wajen wani aiki daban, sai dai tana goyon baya da kuma darajta manufofin kungiyar ta IPOB saboda ra’ayin al;ummar yankin Biafra ne kafar kungiyar ta IPOB.

“Dakarun Yankin Biafra BNG bata daukar umari daga kungiyar IPOB saboda IPOB na aikinta ne daban, sai dai idan bukatar hakan ta taso kasancewar IPOB na wakiltar dukkanin al’ummar yankin Biafra ne.

“Mu Dakarun Yankin Biafra BNG na daukar nauyin kare yankin kasar Biafra, kuma mu baruwanmu da dukkanin wata lambar ta’addanci da Nigeria zata baiwa yankin gabashin kasar, amma sun kwana da sanin cewa ya zamar mana dole mu kare rayukanmu kamar yadda kundin tsarin majalisar dinkin duniya na 2007 ya tanadar.

“Kamar dai kayi misali da wani jami’in Rundunar Sojin Nigeria daya kammala karatun sa, ya fara rayuwa irin ta ‘yan Birni, yazo rana tsaka ya sanya wata kungiya dake fafutukar neman yanci cikin rowan sanyi a matsayin kungiyar yan ta’adda, kowa yasan wannan ai wata tatsuniya ce kawai – Kasar Nigeria ta zamo abar a kalla ayiwa dariya.

“Zaucewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta shafi rundunar sojin Nigeria da har suka tsaya suna furuci cikin nuna tsantsar tsana da kiyayya mai maikon yin Magana mai tattare da hujjoji ko sanya tunani a ciki.

“Abin dariya ne idan aka duba tsawon lokacin da majalisar dinkin duniya ta dauka kafin ta sanya kungiyar Boko Haram daga cikin jerin kungiyoyin Ta’adda amma har wani rikitaccen soja zai zo cikin kankanin lokaci ya sanya kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

“Aniyar rundunar sojin Nigeria zata koma mata ne don kuwa mu ba za’a yaudare mu ba, zamu tashi tsaye don kare rayukanmu ta kowane hali kuma zamu dawo da martaba ta yankin Biafra saboda mu dakarun neman yancin kai ne.

“Ya zama wajibi gwamnatin Nigeria da Dakarun sojinta su koma makaranta don sake karatu kan tarihi. Ya zama wajibi a koyar dasu cewa Nelson Mandela bai taba zama d’an ta’adda ba; Martin Luther King da kuma Mahatma Ghandi bas u taba zama ‘yan ta’adda ba.

“Ya zama wajibi a koyar dasu darasi kan cewa babu wata kungiya ko wani mutum tilo dake fafutukar neman yancin kai da aka taba mannawa lambar ta’addanci; sai dai hakan ya yiyu a kasar da aka taru aka hada ta wai Nigeria.

“Ya Kamata  Gwamnatin Nigeria da Dakarun Sojinta su tafi kasar Burtaniya UK su tambaye su dalilin da yasa basu taba yiwa kungiyar Scots lambar zama ‘yan Ta’adda ba, haka zalika su je kasar Spain don jin labarin Kungiyar Catalonians. Shin wai dole ne sai Nigeria tacio gaba da tozartar da kanta a idon duniya; shin Nigeria wata duniya ce da tai daban da Duniya ta zahiri?

“Buhari da Burtaniya su sani cewa basu isa su yaudare mu ba; idan har zama masu neman yancin kai na nufin zama yan ta’adda, to kuwa muna alfahari da zama ‘yan ta’adda.

“Idan har zama dan yankin Biafra na nufin zama dan ta’adda, to muna farin cikin kasancewa yan ta’adda amma a bias gaskiyar harkokinmu, mu ba yan ta’adda bane, kuma ba zamu taba zama ba.

“Mu yan asalin Biafra ne, mun haramta ta’addanci; al’adunmu da dukkanin abubuwan da muke wakilta sun haramta ta’addanci. Rundunar sojin Nigeria na kashe mana jama’a don haka ya zama dole mu kare kawunanmu don gujewa karewa daga doron kasa.

“Dakarun Yankin Biafra BNG ba zata taba yin amfani da fararen hula ba amma zata fuskanci duk wani mai rike da makami daga rundunar sojin Nigeria.

“An sanya mu a matsayin yan ta’adda ne don basu dammar nuna kabilancinsu akanmu, amma zamu kare kawunanmu. Kada gwamnatin Nigeria ta taba tunanin samun kariya don kuwa kungiyar ba zata taba mika wuya ba har sai idan rai yayi halinsa

“Kasar Burtaniya ce silar dukkanin abun day a faru, sune ke goyon bayan Nigeria akan nuna tsantsar kiyayyar kafa yankin Biafra.

“Burtaniya bata iya sanya kungiyar dake fafutukar kafa yankin Scotland a matsayin kungiyar yan ta’adda ba, amma sun samu dammar tursasa Nigeria daukar kungiyar IPOB wacce take kamar Scotland a matsayin yan ta’adda. Ya zamar mana dole mu dakatar da faruwar wannan shirin kakkabe jinsinmu da ake kokarin yi, Allah ma ba zai yafe mana ba idan har muka tsaya muna kallo aka karar da al’ummar Biafra.”

Idan har ba’a manta ba, a baya bayan nan ne dai Rundunar sojin Nigeria ta sanya kungiyar IPOB a cikin jerin kungiyoyin Ta’adda. Shelkwatar tsaro ta kasa tace biyo bayan bincike da rundunar soji tayi dangane da dukkanin harkokin kungiyar, rundunar sojin ta yanke hukuncin daukar kungiyar IPOB  a matsayin kungiyar ‘yan Tada kayar baya.

No comments:

Post a Comment