Thursday, 14 September 2017

Lokaci Yayi Da Zakusa Ma Karenku (Nnamdi Kanu) Linzami Daga Amiru Danamarya


Da farko dai banso ace abin yakai haka ba, domin nasan irin halin mutanenmu basa daukar komai da wasa, dagaske suke yinkomai ko na kirki ko na banza.

Tun farkon bullar wannan kanu,  tunbayan cin zaben shugaban kasa muhammadu buhari, nayi tunanin masu ruwa da tsakin yakin dayake  babatun karewa zasu fito su nisanta kansu dashi,  suja mashi kunne, su gayamashi cewa wannan tsari daya biyo ba me bullewa bane yama kiyayeshi tun da wuri,  amma a rashin dacewa da samun mutane masu irin tunanina awancan yanki yasa sammm suka nuna halin ko in kula suka barshi yaci gaba da cin karensa babu babbaka.
Wannan sakaci ne ya haifar da halin da muke ciki yanzu tundaga bude gidan radiyon biyafura har yazuwa kamashi, da sakoshi da zanga-zanga matasa mara ma'ana, masu cutar da mutane.

Abinda yaja hankalina yanzu dayasa dole ince wani shine abinda ya faru kwanannan na kaima hausawa mazauna yankin dasuke cewar nan ne kasarsu ta biyafura hari suna kashesu suna kona masu dukiyoyi.

Nayi tunanin igbo sunyi karatun ta nutsu su kula cewa idan wannan abun na kaima yan'uwanmu hari shine suke ganin hanyar da zata sa abasu kasar biyafura, to lallai basu ba kasar biyafura har abada kuwa,  domin idan anci gaba da kone-konen nan har takai mutanen arewa suka tashi dan maida martani to inyamurai sune zasuyi asarar dukiya fiye da kashi 80% cikin 100 na dukiyar da za'a asara yayin wannan arangama,  inya murannan dukiyoyin su ne cike da kasuwannin mu,  da lungu da sako na kauyukanmu, amma kash saboda daqiqanci da jahilci irin nasu sun kasa fahimtar haka, su fito su nisanta kansu da wannan kanun nan,  gomnoninsu su hanashi shiga jahohinsu domin kare dukiyoyin yan'uwansu dake kasuwanci dukkan lungu da saqo na arewacin nigeria.

Idan dai har saboda hadin kai da tunanin bazasu kwarema dan'uwansu baya ba ya sa sun kyaleshi yana iskanci to, mu yan arewa ba cima zaune bane, muna da abincin da zamuci har nan da shekara biyar, dan haka mu ba tsoran araba kasar nan muke, ko yau akace za'a jefa kuri'ar raba gardama to ni zanzabi a rabata kowa ya kama gabansa susha mansu, muci doyarmu, masararmu, dawarmu, wakenmu, shanunmu da dukkan abinda muke nomawa, har ake tunkaho da najeriya na ciyar da afrika, mainakon ace arewa na ciyar da afrika. 

Dan haka lokaci yayi dazamu bude idonmu, duk shegen dayace mana kule muce ma shege cassss, 

Amiru Danamarya


14-09-2017

No comments:

Post a Comment