![]() |
Hon Ismail Yandaki (Wakilin Sanata Umaru Kurfi |
Sanatan ya raba kayan abinci na kimanin N1,200, 000 ga al'ummar Inwalar jangefe dake cikin mazabar Jino cikin karamar hukumar Batagarawa da iftila'i ya fada mawa na iska da ruwa wanda yayi sanadiyar faduwar gidajensu da dama.
Kayan
abincin sun hada da shinkafa buhu ashirin,masara buhu ashirin,gero buhu ashirin
da jarkar olga guda biyar.
Raba kayan
kayan ya samu wakilcin masu taimaka masa daga cikinsu akwai Alh. Muntari Dabo
da Hon. Ismail Usman Yandaki.
Sun samu
tarba daga shugaban jam'iyyar Apc na karamar hukumar Batagarawa Alh. Bala Garba
Tsanni tareda Magaji Jino da sauran masu fada aji na yankin.
Wadannan
bayin Allah da aka kaima wannan tallafi sun nuna godiyarsu tareda addu'ar fatan
alheri ga Sen.Kurfi Allah ya kara mashi jagoranci.
No comments:
Post a Comment