Sanata mai wakiltar katsina ta tsakiya Senator Umaru Kurfi [Nzeribe] ya raba kujeru da tebura na karatu ga Makarantar ‘yan mata watau (Government Girls Day Secondary School) da ke Karamar hukumar Kurfi.
Sanata Kurfi wanda ya samu wakilcin Hon Ismail Yandaki wajen
kaddamar da bada kujerun da tebura ga hukumar makartar a Kurfi.
Hon. Ismail Yandaki ya jaddada cewa mahimmancin ilimin diya
mace na da amfani ga al’umma gaba daya.
Hon. Yandaki ya kara da cewa ganin irin kalubalen da daliban
ke fuskanta wajen amsar karatu wanda rashin abun zama ya jaza koma baya wajen
fahimta da natsuwa ga su daliban a sanda ake koya masu karatu.
Sanata Umaru Kurfi ya bada gudunmuwar kujeru da tebura guda
200 wanda aka saya akan kudi Naira miliyan ukku (N3Million) domin kawu karshen
matsalar wajen zama ga Makarantar dalibai na mata dake karamar hukumar Kurfi.A na ta jawabin, shugabar Makarantar Hajia Rabi Kurfi ta mika Godiya ga yadda Sanata Umaru Kurfi ya magan ce masu matsalar wurin zama da dalibansu ke fuskanta.
Tayi kira ga sauran shuwagabanni da su koyi da irin yadda Sanata Kurfi ke iyakar kokari wajen bunkasa harkar ilimi a duk sanda aka bukaci hakan.
Daga karshe shugaban Kungiyar iyaye na Makarantar Lawal Shafiu ya jajin tawa Hon. Ismail Yandaki da irin yadda yake kai kuken su ga Sanata a duk san da suka bukaci haka.
A karshe yayi Godiya ga Sanata Umar Kurfi bisa gudunmuwar
kujeru da ya tallafa wa Makarantar mata dake Kurfi da kujeru da teburan karatu
don amfanin daliban Makarantar.
No comments:
Post a Comment