Abin mamaki shine yanzu mutane sunzama wani abu daban domin yau idan kabiye wa jamaa sai karasa abinda zakayi yayi daidai dalilina kua shine tsawon shekara daya da wata sha daya da kwana ashirin da hudu ina cikin gwamnatin APC kuma ina bada gudun mua dai dai abinda zan iya.
Cikin wannan tsawon lokaci babu inda zaka ganni naci ma wani mutunci koko an hada kai dani anyi ma wani cin mutunci amma duk da haka ni bantsira ba daga cin mutunci ba.hakan kuma baisa na canza ba dalilin haka kullum sai cigaba nike gani domin Allah yasan abinda ke zucia ta.
To yau kuma domin nayi abinda Allah yace inyi
sai gashi kowa yana fadin albarkacin bakinsa maana wasu suna yabawa wasu kuma
suna aibatawa kai wasu ma harda sharri gamida kazafi.
To ni abinda zance shine farko dai dukan
abinda nayi nabi umar nin Allah ne kamar haka Allah shi yace kabi hakkinka duk
inda yake haka kuma shi yace muso yan uwanmu musulmi kuma mu mutunta junanmu
koda munsamu rashin fahimta da juna.
Saboda haka ninayi abinda naga shine daidai
saboda haka wannan baya canza ni daga dan APC kuma yaron Maigirma gwamna kuma
masoyinsa domin kuwa kullum abinda yake fada mana shine kada muciwa kowa
mutunci kada mu wulakanta kowa saboda haka ni nayi abinda kullum ake horona
dashi.
Daga karshe ina kira ga mutane wadanda suke
ganin banyi masu daidai ba suyi hakuri wannan bayada alaka da siyasar danike
umar nin Allah ne nabi nagode.
Daga naku Hon.Tanimu sada Saad ssa special
duties to his Excellency katsina state governor Rt.Hon.Aminu Bello masari.
No comments:
Post a Comment