Da Farko dai dole in danyi waiwaye akan yadda wannan gwamnatin tazo inyi matashiya da irin halinda Al-umma ta tsinchi kanta a ciki.
Kafin zuwan wannan Gwamnatin wata gwamnatinche akai wadda Al-umma
suka dora ko aka doramasu ta hanyar yin zabe, tundaga shekarar da aka koma
mulkin damakaradiyya a nigeria Jamiyyar PDP ce take mulki a Jahr Katsina har
zuwa Shekarar Dubu Biyu da Sha Biyar inda Al-umma tayi tashin Farin Dango daga
wac...cen
Jamiyyar zuwa Jamiyya mai Mulki a Yanzu wato APC.
Bazamu yi Butulchiba wajen Fadin cewa Jamiyyar data gabata takawo
cigaba a Jahar Katsina a Fannoni daban daban duk kuwa da cewa akwai zarge zarge
na yin Al-mundahana da Dukiyar Al-umma nan da chan, amma haka bazaisa mu rufe
Ido muche Jamiyyar batayi komai ba, akwai kura kurai da sukayi wanda suka sa
Jamaa suka kaurache masu lokacin zabe suka zabi Jamiyya mai Mulki a Yau.
To da alama itama Jamiyyar mai Mulki tana kan hanyar maimaita wasu
daga cikin irin Abubuwan da suka sa aka kaurachema waccen gwamnatin aka zabeta.
Gwamna da Masu taiamakamasa a harkar Mulkin Jamaa.
Idan mukayi duba da yadda gwamnati take tafiya zamu ga cewa Shi
gwamna yanada kishin yaga yayima Al-ummar Jahar Katsina Aiki to amma wasu daga
cikin masu taimakamasa lallai kamar sunayi masa zagon kasa ne basa son ganin
gwamnatinsa tacigaba kansu kawai suka sani da Iyalansu basu da niyyar kawo
sauyi a tafiyar wannan gwamnatin.
Your Excellency Shawarata a wurinka shine lokaci yayi da zakayi
sauye sauye wato garambawul a cikin gwamnatinka nasan kana da rahotanni kala
kala daga bangarori daban daban na irin yadda ake ma tafiyarka zagon kasa, to
karka duba kowa ka duba Jahar Katsina duk wanda baya nan sirri suka nuna cewa
baya kishin Al-umma kansa yasani to ayi kakkaba kowa yagane inda dare yayi
masa.
Al-umma basu da shakku akanka to amma kasani cewa duk wani abu da
akayi Mai kyau ko akasin Haka kai ake kallo ba masu taimaka maka ba, Allah
yabaka ikon sauke nauyi da yake kanka Amin.
Muhammed Aminu Kabir
Wannan rubutu ba
ra’ayin Cliqq Magazine Hausa bane illa iyaka na shi marubucin da ya rubuta.
Cliqq Magazine ba ta da hannu a cikin wannan rubutu kuma da kuma duk abun da
zai biyu baya.
No comments:
Post a Comment