Ina ma farawa da yi maku sallama irin wadda addinin musulunci yayi tanadi tare fatan wannan wasika zata isheku cikin kushin lafiya, ina kuma fatan zaku kalli wannan wasika tawa da idon basira ba don komi ba sai don muhimmanci da nike ganin tana dashi musamman gas u wadanda na rubutu wannan wasika domin ceto rayuwar su.
Ita dai wannan budaddiyar wasiqa na
rubuto ta ne domin rokama yaran mu wadanda ke shekarar karshe ta makarantun
sakandire na jihar nan da basu samu dammar cin jarabawar sharefage da ke bada
dama gwamnati ta biya masu kudin jarabarawar kamala karatu sakandire (SSCE) Alfarmar
da ku taimaki rayuwar su, ku biya masu kudin jarabawar nan duk da dai a halin
da ake cikin yanzu kusan an gama da jarabawar WAEC an fara karbar kudaden
jarabawar NECO su samu suyi koda NECO din ne wallahi wannan jarabawar tana da
matuqar muhimmanci a rayuwar su, zata iya zama sila da wani daga cikin su ya samu
damar da zai iya wuce wa makaranta ta gaba domin karo karatu har ya zaman ma
al’umma abun alfahari.
Sbiya masu kudin jarabawar nan kamr
sadaka ce mai gudana domin kuwa duk al’fanun da aka samu ta hanyar wannan
jarabawa wallahi kuna da lada, kunga kenan kun taimake su kun taimaki rayuwar
su, kuma kun taimaki iyayen su ita kanta al’umma ai taimaka mata wajen rage
yawan bata garin yara a cikin gari. Na tabbatar kun san muhimmmanci da ke akwai
a tattare da yin karatu, kun san ribar da ake samu acikin yin karatu kuma kun
sani cewa a irin wannan zamani da muke cikin babu abinda zaka yi ma mutum wanda
yafi ka taimaka mashi ya yi karatu duba da yanda karatun ya zama shine akan
gaba wajen komi day a shafi al’ummar wannan zamani.
Duk yanda wani yake so ya taimake su
anan gaba madamar basu yi karatu ba fa to babu abinda zai iya yi masu illa ya
basu naira dari ko dari biyu wanda baza ta ma ishsu ba ko su ci abincin rana
guda, kuma na tabbata har ga Allah ko anan gaba a rayuwa duk wanda kuka taimaka
har ya samu damar yin karatu ba zai taba mantawa da ku ba har acikin addu’o’in shi.
Duk yanda iyayen yaran nan suke so su biya masu kudin jarabawar nan basu da
hali, kokarin su ma suga sun sama masu abincin dasu ci yau da gobe ba kudin
jarabawar ba.
Akwai takaici ace yara sun share shekara
shida suna zuwa makaranta amma anyi masu wannan jarabawa ta share fage
(Qualifying Exam) amma sun fadi sai dai kuma yafi zama abin takaici idan akace wadan
nan shekaru shidda sunyi su ne amma hakanan zasu tafi ko takardar tsire ba a
basu ba (ba testimonial balle results) babu wata takarda da zata nuwa cewa
sunje makarantar babbadr sakandire. Kuma tabbas wannan ka iya zama barazana ga
al’umma domin kuwa mayi yawan wadanda ke ba al’ummar mu matsala sune irin
wadanda basu kamala karatun sakandire ba.
Ina fatan zaku yi amfani da damar da
Allah ya baku domin cewa wadannan bayin Allah da al’umma baki daya domin biya
masu kudin jarabawar nan.
Comrade Mubarak
Jibril Yankyaure
talk2yankyaure@yahoo.com
Wannan rubutu ba
ra’ayin Cliqq Magazine Hausa bane illa iyaka na shi marubucin da ya rubuta.
Cliqq Magazine ba ta da hannu a cikin wannan rubutu kuma da kuma duk abun da
zai biyu baya.
No comments:
Post a Comment