![]() |
Amina Bishir |
Cliqqmagazinehausa.com
tayi tattaki zuwa wajen ita yarinyar/dalibar
da kuma Makarantar su yarinyar domin jin gaskiyar abun da ya faru.
Amina Bishir sunanta kuma dalibace a
Katsina College Katsina wanda yanzu haka ajin ta ukku (SS3 Art 5) ta baiyanama
wakilin jaridar Cliqqmagazinehausa.com yadda
abun ya faru kamar haka
“Ina cikin aji ina rubutu, sai Mallam ya
shigo wanda aka fisani da ‘Daddy’, shi Daddy ba Malamin mu bane amma ya kasance
shi ke duti a ranar da abun ya faro. Ya same ni ina yin rubutu na darasin
tarihi [history], ya tambaye ni me nake yi wanda nace masa rubutu nake yi, sai
ya ce ma kawata ta goge jan baki da tasa. Ya juya ya tafi kenan, sai ya ce mani
na kalli ita kawata dake kusa dani nayi mata dariya, wanda nace masa ni bazanyi
ba gaskiya.
Sai ya umurce ni da na tashi na fita
waje na tsugunna [kneel down], Kafin nafita daga cikin ajin sai ya fara buguna
da bulala ta dorina, har na sauka kasa yana buguna, Allah yasa akwai ma’aikatan
ma’aikatar ilimi sun zo tanttan cewa da suke yi, wanda daya daga cikin mutanen
ya ce mashi ya zaka rika bugun diya mace haka da bulala, da dai suka ga ya ki
barin buguna, sai suka karbi bulalan daga hannun shi. Duk da haka sai ya cire
takalminshi yashi gaba da kwada mani shi akan kaina. Dana ga baya da alamar barin
buguna sai nace mashi wallahi idan bai bar buguna zan gayawa iyayena domin su
biman hakkina. Sai yace dani inje ‘yan gayama duk wanda zan gayamawa.
Ciwo Da Malamin ya Jimata Saboda Bugun da yamata |
Ciwo da tabo kenan na bugu a hannun Amina sakamakon bugun da malami yamata |
Kwatsam sai Mallamin yace shi wallahu sharri
ne/Kazafi ne ake mashi, ma’ana da maganata da ta shugaban ajin tamu ba gaskiya
bane.”
Da wakilin Cliqqmagazinehausa.com ya tambaye ta ko mai yasa bata je makaranta
ba “sai tace ai an dakatar da ita sai ranar litinin aka ce ta dawo makaranta”.
Daga karshe ta jaddada mana cewa ba it
aba ne ta shafa janbaki ba, kawarta tace wadda take zaune kusa da ita tashafa. Sannan
kuma tace duk ‘yan ajinsu zasuyi shaidan abun da ya faru.
Da kuma wakilmu ya ziyarci Makarantar su Amina domin jin nasu bayanin akan abun da ya faru. Cliqqmagazinehausa.com ta samu tattaunawa da maitamakin shugaban Makarantar [Vice Principal Administration] Mal. Musa Makudawa yayi bayani kamar haka;
Tabon Bugu a kafadun hannuta kenan |
Da kuma wakilmu ya ziyarci Makarantar su Amina domin jin nasu bayanin akan abun da ya faru. Cliqqmagazinehausa.com ta samu tattaunawa da maitamakin shugaban Makarantar [Vice Principal Administration] Mal. Musa Makudawa yayi bayani kamar haka;
“Abun da yafaru tsakanin dalibarmu da
kuma malamin mu watau Mallam Daddy abu ne wanda duk mai kishin ilimi da kuma
koyama yara dalibai da’a dole ya kyamace abun da Amina Bishir tayi. A bisa
bincike da muka yi karkashin kwamitin horaswa [discipline committee] ya nuna
cewa Shi Malamin ya kasance shi ke duti a Makarantar, sannan ya shiga ajin su
Amina sai yaga tasaka jan baki wanda kuma a dokar makaranta bai kamata tasaka
ba, kaga tun a nan ta saba ma dokar makaranta, sai ya umurce ta data goge shi
sannan kuma ta juya ta kalli dalibar kusa da ita tayi mata murmushi don taga
tabbas ko jan bakin ya fita, ya juya kenan zai tafi sai yaji Amina tace ubanwa
zai goge, bazan goge ba. Kalmar zagin tayi mashi ya bata mashi rai har yadauki
matakin bugunta da bulala.
Sannan ‘yan kwamitin Horaswa sun kira ta
kuma ta amsa laifin ta har suka mata fada suka jamata kunne da kada ta sake
aikata wannan abu da tayi”.
Da wakilin mu ya tambaye shi ko
makaranta ta dakatar da Amina daga zuwa aji sai yace mani “Makaranta bata daka
tarda ita ba amma sun kira ta sun bata takardar gaiyatar mahaifinta domin yazu
makarata.”
Mallam Musa yace Baban ta bai samu damar
zuwa ba sai dai Yayanta wanda ya wakilci baban. Kuma ya ba hukumar makaranta
hakuri akan rashin kunya da kanwarsa tayi ma Malamin.
To kunji abun da yafaru tsakanin Daliba
Amina Bishir da mallaminta Daddy. Shin ko ya gaskiyan maganar zata kaya, wannan
kuma sai mun samu shaidu ‘yan ajinsu Amina Domin mu ji ta bakin su.
Yanzu Haka Amina bata san sakamakon ta
ba gashi kuma har ta zu baban aji na Ukku (SS3) wanda daga shi ta kamala makaranta.
Amma kuma Mal. Musa Makudawa ya ambaci
cewa Amina ba zaman da ake bada makarantarsu ba tayi rijistar jarabawa, Kenan
Amina ba Daliba bace a Katsina College Katsina ga yarda yake nufi kenan.
Bisa GA dukka alamu akwai zalunci cikin wannan bayani, ayi kokarin zantawa dasu bakin da suka kawo ziyara na ma'aikatar ilimi sannan yan ajinsu dalibar. Na samu shakku ne bisaga korafe korafe da nake samu ga dalibai na cikin jihar nan.
ReplyDeleteba adalci
ReplyDeleteKai, wannan abin da salka salka a cikin wannan sha'anin.
ReplyDeleteYa kamata a nada kwamiti mai zaman kan shi, domin a gano gaskiyar abinda ya faru. Ni kam ra'ayi na kenan.