Thursday, 2 March 2017

Wani Malami Ya Fasa Jikin Daliba Da Bugu A Makarantar Katsina College Katsina Don Ta ki Mashi Dariya


Cliqqmagazinehausa.com ta samu labarin wannan abun takaici daga shafin Abdullahi Hassan na Facebook. Amma tabbacin labarin bai ida samuwa ba har lokacin buga wannan wasika da mai rubutun ya rubuta a shafin shi. Amma wakillamu na iya kar Kokarin bin ciko wannan lamari don yin gaskiya ga wanda aka zalunta.

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA KWAMISHINIYAR ILIMI TA JIHAR KATSINA.

Prof. Halimatu Sa'adiya.

Assalamu Alaikum,

Gaisuwa da fatan alheri gareki ya maigirma kwamishina hakika ina cike da damuwa da takaici yanda ake gudanar da harkar ilimi a jihar nan musamman bangaren tarbiyya tsakanin malamai da dalibai, Kokena gareki da shawara ga wani abu da yafaru a makarantar KATSINA COLLEGE KATSINA SENIOR SECTION (FEMALE) wadda yanzu suke da matsugunni a GOVERNMENT COLLEGE KATSINA tsakanin 12:30pm-5:30pm tsakanin wani malami da aka boye mana hakikanin sunan sa saidai laqabinsa MALAM DADY (CHEMISTRY) da wata daliba mai suna AMINA BISHIR (SS3 ART 5).

ABINDA YAFARU.

Jiya talata 28/02/2017 malami mai lakabi da Malam Daddy yashiga ajinsu lokacin da malaminsu na history yake masu darasi ya zagaya don ya duba masu note da wadanda basuyi yana bugun wadanda basuyi ita kuma kamar yadda aka samu shaidar ta ya isketa tanayi amma duk da haka ya nemi janta da wasa wai don yaga fuskar ta a daure shine ya umurci ce data yima ta kusada da ita dariya wadda ita batayin note din bayan ya bigeta, Ita kuma batayi ba wannan yajaza ya fiddo ta ya dinga bugunta da bulala bayan malamin da yake koyamasu ya rike sa yana bashi hakuri yasa takalminsa yadinga bugunta wanda yajaza yaimata bugun da ya wuce wuri a fahimta ta Inda ya farfasa mata jiki.

Bayan dowowar ta gida iyayenta sukaga irin bugun da yaima diyarsu suka garzayya da wakilinsu zuwa makarantar don jin gaskiyar abinda yafaru saboda kauce ma jita jitar yaron zamani wanda nine wanda na take ma yayan yarinyar baya shugaban makarantar ya amshe mu cikin mutunci da girmamawa kuma ya aika aka kirata donjin daga gareta yaji Inda ya mika case din ga mataimakansa mace da namiji don yin bincike agane gaskiya amma Kass Allah bai hure masa abokan aiki ba wadanda basu san ya zasu saurari mai korafi ba suka hau mu da fada amma dai muka matsa a bincika aka kuma bincika tare da shaidu abinda ta shaidama iyayenta gaskia ne a cikin Shawarwarin da aka basu na Baikamata ace malami ya tsaya wasa da dalibansa ba wanda haka ke jaza raini a tsakani kuma bamu sani ba ko akwai wata doka data bada damar malami yace dole sai dalibi ko daliba taimasu dariya a matsayin su na abin koyi ga dalibai hakan baidace ba, Nasan wajibi ne dalibi ko daliba data ko ya Saba doka ta aji, makaranta, ko hukumar ilimi dole a hukunta shi ko dan wanene amma sabanin haka badaidai bane amma mutanen nan V. C Adm & V. C Acad suka rasa fuskar dazasu yimana magana Mai dadi koda yarinyar ce Keda laifi abinda ake cema manner of approaching hakan yajaza hayaniya tsakanin mu dasu, Abinda na fahimta wasu makarantun suna da wani tsari na rashin amsar kuskuren maaikatansu da amsar shawara da ake basu inko basu amsar shawara banga dalilin yin kungiyar iyaye da malamai.

RASHIN SANIN MAKAMAR AIKI.

Wasu daga cikin abubuwan da wadannan mutanen suka aikata :
1.Rashin saurarar mai koke in yazo dashi.
2.Rashin iya maida ma mai koke magana.
3.Kokarin boye laifin malami.
4.Rashin tsawata ma malaman musamman matasa Masu karancin Shekaru.

KIRAN MU AMAMADIN IYAYEN YARINYA.

Yazama wajibi hukumar ilimi tayi bincike kar ta yi amfani da abinda muka fadi don hukunta mai laifi kowaye yin hakan shine adalci adalci kuma na dawamar da shugabanci yai nasara yasa daukaka tunda hukumar makaranta wakilan ta basu da manner of approach, yakamata ayi gyara bangaren malamai musamman matasan malamai Masu karancin shekaru wajen yanda suke mu'ammulah da dalibansu musamman mata abune kowa ya sani irin yanda abin ke gudana babu dadin ji inba diyar ka akwai kanwar ka a cikin makarantun nasan kunaji labarin yanda rashin kamun kai da natsuwa ke wakana tsakanin malaman matasa da daliban musamman mata inba kaji ba ko gani ka ziyarci wata makarantar gwamnati kagani abun akwai gyara bangaren tarbiyya wanda mafi akasarin daliban dama suna zuwa da tasu rashin tarbiyya amma inbasuga fuska ko kofa ba to lamarin zaizo da sauki amma da dama wasu malaman suke bude ma dalibi ko daliba kofa kodai adinga jansu da wasa ko ace ana son su ko wata mu'ammulah ta banza su shiga tsakanin malami da Dalibai hakan najaza raini da lalacewar tarbiya amma duk malamin da ya kama kansa to bazai ga raini ba, inma ta rainashi to yanada da damar hukunta ta Shima hukunci asan wanda zaiyi kar abun ya wuce waje saboda wani hukunci yana wuce waje musamman mata.

Lallai yakamata maaikatar ilimi ta waiwaiyi wannan matsalar don kafa doka da daukar mataki Don inhar zaasa ido a kyale to wani inyayi hakuri wani bazai ba hakan na iya jaza daukar doka ga hannu wanda hakan zai haifar da matsala cikin alummar mu, Kuma Yakamata a kara baiwa wasu malamai horo na musamman bangaren yanda suyi mu'ammulah da dalibansu a makaranta da wajenta Don gaskiya mu'ammulah akwai gyara sosai sannan iyayen yara su zage damtse wajen baiwa yayansu tarbiyya mai kyau kuma da nuna masu mahimmancin malami ga alummah.

Akarshe muna fatan maigirma kwamishiniyya zata duba wannan lamari da kyau don kaucema abinda zai biyo baya da kuma rushe harkar ilimi a jihar.

Kihuta lafiya.
Abdullahi Hassan Katsina.

 

5 comments:

  1. Gaskiya yakamata Commissioner Ilimi ta binciki ainahin gaskiyar AL'amari domin tabbatar da gaskiya. Malami: malami ne. Dalibi: Dalibi ne.

    ReplyDelete
  2. wannan Magana gaskiya ce domi dukkanin nasara tana tare da gaskiya

    ReplyDelete
  3. wannan Magana gaskiya ce domi dukkanin nasara tana tare da gaskiya

    ReplyDelete
  4. An biyashi albashi a ranar kuwa? Wlhy malamai mutane ne Kamar kowa, sunada bukatu da matsalolin rayuwa kamar kowa. Ina bada shawara ga shugabanni don Allah su duba matsalar kyautata yanayin aikin malamanmu. Allah yasa mudace

    ReplyDelete