Monday, 23 January 2017

Kwamitin Biyan Kudin Gratuti Yara Fara Zaman Tantancewa A Katsina


A yau ne committee na biyan gratuity wanda H.E Aminu Bello Masari ya kafa a karkashin jagorancin Alhaji Umaru Adamu, ya fara zama a Katsina state secretariat.

An dorawa kwamitin alhakin tabbatar da biyan gratuity na ma'aikatan jaha da local governments.

Indai ba'a manta ba a shekarar bara anyi irin wannan biyan inda gwamnatin jahar katsina ta biya kudi naira bilyan goma sha daya ga ma'aikata a matsayin kudin gratuity , cikin ikon allah bana ma gashi za'a ci gaba daga inda aka tsaya.

Kwamitin dai zai duba da kuma tabbatar da cewa ma'aikatan jaha, karamar hukuma da L.E.A  da suka haura dubu hudu (4000) sun samu kudinsu na ajiye aiki ba tare da wata tangarda ba.

Kwamitin wanda ya kunshi gogaggin ma'aikata kamar su Alhaji Ibrahim Dabo Bujawa, SA Radio monitoring Mansir Ali Mashi, sai kuma Auditor General na jaha dana local government ya fara aikinsa.

Kuma ana tunanin zai tantance ma'aikatan domin biyan zunzurutun kudi naira bilyan bakwai da miliyan dari hudu.

 

No comments:

Post a Comment