Thursday, 12 January 2017

Tunanin Zuci. Daga Mansur Halilu


Ina ma dai a ce dukkanin Gwamnonin Arewa, za su nemi wannan Littafin su bai wa dukkanin 'Daliban Azuzuwan 'Karamar Sakandare da ke Jihohinsu, musamman ma, a daidai lokacin da aka koma Hutunnan.
 
Idan Gwamnonin na Arewa sun kasa domin rashin sanin ko ma akwai Littafin, ko kuma don ba wannan ne abin da ke gabansu ba, ko kuwa don shi kansa ma Harshen Hausar bai dame su ba, ina kira ga dukkanin Iyayen yara 'yan Makaranta, Musulmai ne ko kuwa Kiristoci, Hausawa ne ko kuma 'yan wata 'Kabilar ne, a kan su yi 'ko'kari su nemi wannan Littafi mai suna; "Ilimi Hasken Rayuwa" domin amfanin Rayuwar Ilimin 'Ya'yayensu masu Albarka da ke karatu yanzu, a matakin Sakandare, musamman 'Kananan Azuzuwan Farko Guda Uku!
 
Rashin Mallakar Littafin nan ga 'Dalibai 'yan Makaranta da ke Jihohin Arewa Guda Goma sha Tara, inda aka hukunta koyo da kuma koyar da Harshen Hausa, a matsayin Darasin Dolen Dole, ba 'karamin ci baya ba ne ga Karatunsu na Darasin Harshen Hausa, wanda kuma Dolen Dole ne a kan kowane 'Dalibi ko da Littafi kuma ko babu, a irin yadda yake a Constitution ɗin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya!
 

No comments:

Post a Comment