Saturday, 7 January 2017

Dalilan Da Ya Sa Muka Kafa Kungiyar Masari Restoration Awareness Forum- Inji Shugabanta Alhaji Sabo Musa

Sabo Musa

Alhaji Sabo Musa Hassan Katsina Gogaggen dan siyasa ne, kuma Shi ne Shugaban Kungiyar nan na Masari Restoration Awareness Forum. Wadda ta kudiri aniyar wayar da kan jama'a kan Ayyukan Gwamnatin Aminu Bello Masari ke gudanarwa a Katsina. A tattaunawarsa da Rariya a Katsina ya fadi dalilin da ya sanya suka kafa kungiyar, inda suke samun kudin tafiyar da ita, da kuma wasu muhimman batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance:-

Daga Jamilu Dabawa

Rariya: Masu karatu za su so jin dalilin da yasa ku ka kafa wannan kungiya a dai-dai wannan lokaci?

Sabo Musa: Kungiya ce da take fadakarwa, da kuma wayar da kan al'umma kan ayyukan hazikin gwamnanmu Malam Aminu Bello Masari. Ya yi ayyuka sosai na dan lokacin nan da ya hau na qasa da shekara biyu nan, amma sai muka fahimci cewa mutane ba su fahimci ayyuka da aka yi ba, inda har wasu ke samu damar sukarta a kafafen watsa labarai da kuma shafinka sada zumunta na zamani suna cewa babu abinda aka yi.
Kamar Yadda Masari ya iske asusun gwamnatin jaha da kuma matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar, har yake biyan albashi da yan fansho kan kari da biyan kudin sallama aiki da biyan kudin daliban dake karatu kasashe ketare. Ga kuma gyaran makarantu sama da 2000 da kuma gina sabbi, gyaran manyan asibitocinmu na Funtua, Daura da Katsina domin maida su na zamani. Gwamnati ta na kokari wajen ganin an bunkasa harkar noma, samar da ruwan sha, samawa matasa ayyukan yi, inganta harkar tsaro da kuma habbaka tattalin arzikin jahar.
Wadanan dalilan ne yasa muka ga ya dace mu kafa wannan kungiyar; domin kara wayar da kan jama'a da fadakar da su kudurorin mai girma gwamna da kuma ayyukan da yake yi. Inda Nan gaba kadan so muke ko talla ka ke bisa baro idan an tambaye ka mi gwamnatin masari ta yi za ka iya bada amsa.

Rariya: Da kafa wannan kungiya zuwa yanzu; wadanne ayyuka ku ka gudanar domin fadakar da kan al'ummar jahar Katsina kan ayyukan da Gwamnatin Aminu Bello Masari ta yi?

Sabo Musa:Mun je gidajen rediyo mun gabatar da shirye shirye daban-daban domin fadakarwa da ilmantarwa kan ayyukan wannan gwamnati. Haka kuma a kafafen sadarwa na zamani kamar su whatsapp, facebook, twitter duk muna ta tallata ayyukan wannan gwamnati. Har ila yau, idan wani ya kalubalanci wannan gwamnati mu kan ba shi amsa tare da kwararan hujjoji na zahiri. Kuma nan gaba kadan za mu bullo da wadansu shirye-shirye na kara fadakar da al'umma jahar Katsina dama duniya baki daya na ayyukan alheri da Gwamna Masari ke aiwatarwa.

Rariya: Ta wace hanya ku ke samun kudin tafiyar da wannan kungiya?

Sabo Musa: Babu wanda ke ba mu ko sisi, Mu shugabanninta ke daukar nauyin tafiyar da ita. Babu inda muka je wajen wani da ya ba mu wani abu domin tafiyar da ita. Hatta gwamnatin jihar Katsina ba ta ba mu ko naira goma ba har yanzu da muke maganar nan. Kuma babu wanda ya dauki nauyinmu, mu ke daukar nauyinta. Kishi ne da kuma ganin Gwamna Masari mutum ne mai son kawowa jihar cigaba ya sanya muka kirkirota

Rariya: Zuwa yanzu; wadanne irin kalubale ne ku ke fuskanta?

Sabo Musa: Akwai wadansu tsiraru da ba su son asan mai gwamnatin Masari ta yi suna shiga kafafen watsa labarai suna cewa kamar karya ake, ko da wata manufa muka kafata. duk da hotan da muke gwadawa saboda ba su asan me masari ya yi. yanzu daga bude ofishin nan sama da kungiya dari suka kawo mana ziyara kuma muka tallata ayyukan Dallatu a gare su kuma suka gamsu da bayanan da muka yi masu;Tashin hankalinsu don me al'umma za su san ayyuka da Masari ya yi a Katsina.

Rariya:Daga karshe wane kira gareka ga su wadannan mutane da kuma al'ummar jahar Katsina?

Sabo Musa: Kirana shi ne Mutane su zamanto masu adalci mu aje banbanci siyasa. idan Masari ya yi abun alheri a fada. ayi adawa ta adalci da gaskiya. kuma ina kira ga alummar jihar Katsina da su cigaba da ba wannan goyan baya saboda gurin mai girma gwamna ya ciyar da jahar Katsina gaba. Haka suma 'ya'yan jam'iyyarmu ta APC da mu zamo masu hadin kai dai kaunar juna, mu guji abinda zai kawo rarrabuwar kawuna tsakaninmu, manufar dai wadannan shugabanni Allah ba su damar sauke nauyi da ya dora masu. Kodayaushe kofar mu a bude take ga masu ba da shawarwari domin ganin mun samu nasara.

 Asali: Rariya

No comments:

Post a Comment