Wednesday, 28 December 2016

Noma | Gwamnatin Jihar Katsina Zata Yi Taron Habaka Nomar Rani A Jibia LG


Gwamnatin Jihar Katsina, a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, hadin guiwa da Babban Bankin Najeriya (CBN), ta kammala shirye shiryen habaka noman rani, musamman na Shinkafa a fadin Jihar nan.

Kan haka ne Gwamnati take gayyatar al'umma wajen taron kaddamar da wannan shiri wanda idan Allah Ya yarda za ayi gobe Alhamis, 29/12/2015 a filin Noman rani na Madatsar ruwa (Dam) dake garin Jibiya da karfe 11 na safe

Wannan shiri, da yardar Allah zai habaka tare da daga martabar harkar noman rani da kuma tattalin arzikin manoma da kuma Jihar Katsina baki daya.

Muna rokon Allah (SWT) Yasa albarka a cikin wannan shiri, Allahumma Amin.
Asali: SSA Social Media

 

No comments:

Post a Comment