Wednesday, 14 December 2016

Gwamna Masari Zai Maido Tsarin Albashin CONHESS Na Ma'aikatan Lafiya


Gwamnatin Jihar Katsina za ta mayar wa Ma'aikatan lafiya na Kananan Hukumomi da tsarin albashin CONHESS da aka dakatar a watannin baya.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana haka yau a Gidan Janar Muhammadu Buhari, fadar Gwamnatin Jihar Katsina, bayan ya amshi rahoton Kwamin da Gwamnati ta kafa domin tantance Ma'aikatan da suka cancanci amsar wannan tsarin albashi. Ya kara da cewa wadanda aka tantance ne kadai za a mayar mawa kuma biyan zai hada har da ariyas na watannin da su...ka gabata.

Tun farko a nashi jawabin, Shugaban Kwamitin Alhaji Salihu Maigari Danjuma mni, ya bada rahoton cewa Kwamitin wanda ya kunshi har da Shuwagabannin kungiyoyin kwadago, ya tantance Ma'aikata har 8,640 wanda kunshi;

1. 4,811 da suke aiki a asibitoci
2. 2,015 na bangaren samar da ruwa da tsabtar muhalli.
3. 1,038 na bangaren aikin gona
4. 776 na bangaren Ilimi da walwalar jama'a

Haka kuma sun sami Ma'aikata 1,056 wadanda suka rika amsar wannan alawus ba bisa ka'ida ba, a saboda haka sun bada shawarar a mayar dasu kan tsarin albashi irin na sauran ma'aikata.

Haka kuma sun bada shawarar da a inganta tsarin kula da duba asibitocin tare da Ma'aikatan domin kauce ma fadawa cikin irin wannan matsalar nan gaba.

Kwamitin kuma ya bada shawarar cewa duk wani mai dauke da takardar kammala karatu (Statement of result) wadda ta kai tsawon shekara 10 to lallai ne ya kawo Satifiket (Certificate) kafin a yarda da zaman shi Malamin lafiya.
Asali: AA Bawa

 

No comments:

Post a Comment