Saturday, 15 October 2016

WATA MAGANA TA DAWO,WATA MAGANA TA TAFI! Daga Real Bahaushe

Duk da a satin nan na shiga cikin hidimomi sosai masu yawan da na dade ban shiga irin su ba,amma hakan duk bai hana ni dan lekowa kafofi da kofofi ba da shan abin kofunan labarun da ke karakaina ba.

Al'amurran daga ciki akwai batun maganganun Uwargidan Shugaba Buhari,tasiri ko suka ko yabonsu duk abin duba ne,inda na ga da yawan masu sharhi sun kasa kallon bangarori,su dai fatansu su karawa Borno dawaki.


Kamar yadda maganganunta suka zo da mamaki,gaskiyar magana ba a yi tunanin za ta aikata haka ba.Amma mijinta don bai yi wa wahalallun jam'iyya aiki ba wannan ba laifi ba ne,muddin dai sun cancanta kuma sun fi wahalhalun,me ya kawo maganar tsoron bore ko tada jijiyoyin wuya a nan,ko kila ta rasa wasu daman maki ne kuma?


Martanin Shugaba Buhari ga maganar sun sa an sake jin kunya a kasar nan,wasu na cewa ya raina darajar mata, wasu kuma na nuna ya bi sahun gaulan nan Donald Trump wai ya yi batsa,daga baya dai ya nuna wasa yake yi maganar tana kula da falo da kicin da dakunansa kadai!Amma me zai sa ba zai ce haka ba?kwancewa miji zane a kasuwa irin wannan!Gaskiya ko ma mene ne ta saki bakinta da yawa;domin duk abubuwan tsegumi ne ba shawarwari ba,ai yanzu an daina yayin irin wannan duniyar,kuma kowa ya sani dole ne Buharin ya yi irin maganganun nan.


Batu na biyu samun kubuto da Yanmatan Chibok 21,gaskiya ba karamin abin farin ciki ba ne,domin a lokacin da na yi zaman dirshan a Unity Fountain Abuja,sai da na zubar da hawaye bayan ganawa da iyayensu,na sha suka daga wasu cewa kudi muke nema,ko ace siyasa da suka ce,amma Alhamdulillahi mun yi murna tare da jinjina ga shugaban kasa,kuma hakan na nuna alamun nasara a gwagwarmayar da wasu ke ganin kamar kuka ne a dawa,alhalin ko tsangwamar 'Yansanda ma ta isa a sa a daina,godiya ga jaridun da ke yekuwar fafutukar nan da kuma masu sukar #BringBackOurGirls!


Daga karshe zan lullube da harkar tsaro ne da kai wa juna hari mai muni na tarzoma a kasata,gaskiyar magana hatta ra'ayoyin wasu malamai ba na tare da su ko kadan!


Dan'uwa Zakariyya Yunus ya yi wasu maganganu da suka yi matukar burge ni,masu adalci da fede gaskiya,bari na waiwayi me ya fada:


Kamar yadda akidar Shi'a ake sukarta da batun zagin Sahabbai wanda hakan illa ce babba,to fa kuma dole ne a fahimci daukar doka da hannu ma babbar illa ce,domin tarihi an yi shi ne ba don ado ba kadai,a tuno da batun dokar hular kwano da 'yan kungiyar Boko-Haram a Borno mana,a kalli kasashen Iraki da Siriya a gani mana!


Ya kamata a sai ta tunani da kuma ayyuka domin samun dawwamammen zaman lafiya,kada kowa da kowa ya rudar da kowa don Allah.Shiyasa Sheik Bala Lau ya ce duk goyon bayan da suke yi wa hukuma kan Shi'a ba su goyon bayan daukar doka da hannu!


A ciza a busa sannan a hura ba hurin wuta ba!


Real Bahaushe.
08038387516.
kabeerloquacious77@gmail.com.
15/10/2016



Gargadi: Wannan rubutu ba ra’ayin Cliqq Magazine Hausa bane illa iyaka na shi marubucin da ya rubuta. Cliqq Magazine ba ta da hannu a cikin wannan rubutu kuma da kuma duk abun da zai biyu baya.

2 comments:

  1. Kabir Bahaushe, Kayi Tambihi Mai Ma'ana Da Nuna Kishin Kasa, Irin Wadannan Ra'ayoyin Kullun Muke So Mu Rika Gani Daga Matasa Irin Ku A Kullun Inda Aka Ga Gaskiya A Fade Ta Komi Dacin Ta, Inda Aka Kuma Anyi Abin Kirki A Yaba, Wannan Shi Ke Kara Ma Ko Wane Shugaba Kwarin Guiwa, Lallai Maganar Aunty A'i Tayine Kan Wani Son Zuciyar Ta, Da Kamata Yayi Ace Yan Siyasar Da Suka Hade Kai Suka Kafa Gwamnatin Sukayi Wannan Koken Ba Ita Ba, Kawai Ya Hanata Office Din First Lady Shi Take Ji Ma Zafi Karka Dada Kar Ka Raga, Nidai Tawa Fahimtar Kenan.

    ReplyDelete