Monday, 10 October 2016

MALUMFASHI-:|:- AN KAMA TUKUR YANA SA MAGANIN BERA A NIKA


A yau mutanen bayan Nitel suna cikin wani tashin hankali,sakamakon wani mummunan al'amari da yaso ya faru, wani mutum mai suna TUKUR wanda yake zaune a bayan nitel din yaje injin nika da niyyar sayen dusa, bayan yabada kudin dussar sai yasa hannun sa aljihu ya fiddo maganin bera ya barbada a cikin gari na jama'a,.cikin hukuncin Allah sai Mai nikan mai Suna MALAM SANI ya gansa. lokacin daya kama TUKUR da shinkafar beran nan take aka sanar da jami'an tsaro dake MTD MLF.
Da wakilin CLIQQ Magazine a yankin na Malumfashu, Ismail A Sanda yake zantawa da mai injin nikan ya shaida mani cewa nikan daya barbada ma maganin nawani gidane  wanda suka taba tona TUKUR akan satar akuya a can baya,
Shine yabiyo garin nikan su domin yasa masu guba aciki.
Mutanen bayan Nitel din sun kara shaida mani cewar TUKUR bako ne basu san asalin garin suba.ya taba koma wa kirista,daga nan ya koma addinin islama.
Yanzu haka dai TUKUR yana hannun jami'an tsaro na garin Malumfashi.

2 comments:

  1. Allah shi kyauta. Kuma shi kara tona Tukur wani mai mugun kudiri irin nashI.

    ReplyDelete
  2. Allah shi kyauta. Kuma shi kara tona Tukur wani mai mugun kudiri irin nashI.

    ReplyDelete