Tuesday, 20 September 2016

YAN FASHI SUN SACE MALAMAR PRIMARY A ZARIA.

Yan Fashi sun Sace Malamar makarantar Firamare a garin Zaria.


Gungun 'yan Fashi da makami a ranar Litinin din data gabata suka sace wata matar aure mai kimanin shekaru 30 a Zangon Shanu, Zaria.

Matar, Fatima Umar, wacce malamace a LEA Maiduguri dake titin Maiduguri, Kaduna, an sace ta ne a gidan mijinta bayan da yan fashin suka shiga gidan neman kudi, da basu samu ba shine sukayi awon gaba da iya.

Wanda akayi abin a gabanshi yace : "Al'amarin ya faru da kamar karfe 2 na dare. Mijin matar dai lakcara ne a jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zaria. A lokacin da yan fashin suka dudduba ko ina a cikin gidan amma basu samu kudi ba, sai sukayi kokarin sace wani yaro, amma Fatima ta rike yaron ta hanasu daukarshi. Wannan yasa suka kyale yaron suka tafi da ita".

Kamar yadda mutumin ya tabbatar, Yan Fashin sun tuntubi iyalan matar, inda suka bukaci Naira Miliyan Goma kafin su sakota. A Daren jiya da wannan labarin ya riske mu, yarjejeniya na ci gaba da wakana tsakanin 'yan Fashin da kuma iyalan fatima. Inda majiyar ta tabbatar da cewa har an samu rangwamen kudin sun dawo Naira Miliyan Bakwai.

A kokarin tattaunawa da PUBLIC RELATION OFFICER na Kaduna, ASP Aliyu Usman, yace yayi tafiya wajen jahar, amma yayi alkawarin neman ba'asi da tuntubar wannan jarida.


No comments:

Post a Comment