Gwamnan na Jihar Katsina, Rt. Aminu Bello Masari a ranar Juma'ar data gabata, ya baiwa al'ummar Jihar Katsina hakuri da kuma basu tabbaci akan kokarin gwamnati na Samar da ingantaccen Muhallin kula da marasa lafiya a Jihar.
Gwamnan ya yi hakan ne a taron manema labarai da ya gudana a Katsina. Inda Gwamnan ya ce gwamnatinshi ta kudiri aniyar daukar ma'aikatan lafiya Har guda dari shida (600).
Wannan ya kara da cewa: "Mun fahimci cewa malaman lafiyar mu suna samun yawaitar ayyuka saboda karancinsu a asibitocin gwamnati da Clinic."
Ya kara da cewa: "Mun gano cewa da yawa daga cikin malaman lafiyar sun yi Ritaya ko kuma sun bar aikin gwamnatin jaha sun koma majami'o'in lafiya na Gwamnatin tarayya.
" Gwamnatin Jaha zata fara daukar likitoci, Nurses, Unguwar Zoma da sauran ma'aikatan lafiya nan ba da jimawa ba.
"Muna kokarin daukar ma'aikatan lafiya da zasu iya kula da asibitocinmu, bangaren Primary Healthcare, da kuma duk wata Clinic dake fadin jahar.
" Daukar ma'aikatan ya zama dole duba da rashin daukar ma'aikatan da gwamnatin data shude tayi."
Masari yace a halin yanzu dai gyare-gyare da kuma yiwa asibitocin Funtua, Katsina da kuma Daura kwaskwarima na CI gaba da tafiyar kamar yadda aka tsara ta hanyar ruguje inda ya lalace da Gina sababbin wurare.
Ya ce gwamnatin jaha na kan gyaran manyan Asibitocin Dutsinma, Kankia da kuma Malumfashi. A karshe gwamnan ya nemi afuwar mutane tare da neman jama'ar jahar su kara hakuri domin gwamnatin shi na da kudirin gyara sashen ilimi na Jihar.
No comments:
Post a Comment