Sunday, 18 September 2016

WATA RANA, BUHARI SAI YA SA HANNUN AKAN TAKARDAR YIN MURABUS.


SATAR FASAHA: Wata Rana, Buhari sai ya sa hannu akan takardar yin Murabus ba tare da ya karanta abinda ke a ciki ba - Wakilin Fayose. 

Wakilin Gwamna Aypdele Fayose akan harkokin sadarwa na zamani, Mr Lee Olayinka ya nuna sakacin shuga Muhammadu Buhari dangane da satar zancen wani a matsayin abin kunya ga kasar Nigeria.

Wakilin na Fayose, Lere Olayinka yace: "Wata rana, Shugaban Kasa Buhari zai rattaba hannune kawai akan takardar murabus dinshi daga kujerarshi ba tare da ya karanta abinda takardar ta kuna ba.

“Babu wani shugaban Kasa da ya taba kawo irin wannan cin fuskar da abin kunya a idon duniya kamar shugaba Buhari, sannan wannan ba shugaban kadai ya shafa ba, harma da Al'ummar Nigeria baki daya."

"Satar Fasahar wani babban kuskure ne kuma laifi mai zaman kanshi da ya zarce laifin satar kudin gwamnati.

" Nan gaba idan zaku rubutawa shugaba Muhammadu Buhari rakardar zance, Ku rubuta ta a sigar Zanen Katun [CARTOON], a nan zai gane ko satar fasahar wani ce akayi kai tsaye." Mr Lere Olayinka ya fadi hakan.

No comments:

Post a Comment