Thursday, 15 September 2016

TARON MAJALISAR ZARTASWA NA 14:

TARO NA GOMA SHA HUDU NA MAJALISAR ZARTASWA TA JIHAR KATSINA WANDA AKAYI A RANAR 15/09/2016.
Daga: Sani Hamza Funtua: Cliqq Magazine Hausa Editor.
_____________________________________________

A ranar 15 ga watan Satunba, shekarata 2016. Majalisar Zartaswa ta Jihar Katsina tayi taro kamar yadda aka saba a duk bayan shekara, wannan taro dai shine karo na Goma sha Hudu. An tattauna tare da fitar da abubuwan da ake sa ran Gwamnatin zatayi a cikin wannan Shekara.

Abubuwan da aka yarda dayinsu sune kamar haka:


1. Daukar Malaman Makaranta guda 1,900 na Firamare da Sakandire.

2.  Sayen sabon Injin halba ruwa domin inganta hanyar samar da ruwa daga Ajiwa.

3. Sayen Sinadaren tacewa da tsabtace ruwa.

4. Gina (Benaye) karin azuzuwa da dakunan kwana,  gami da kananan dakunan shan magani a makarantun Sakandare na kimiyya dake a Ajiwa da Batagarawa.

5. Gyarawa tare da kafa sababbin fitulun kan tituna domin inganta tsaro da kyautata walwalar al'umma.


Cikakken bayanin ayyukan zai biyo baya in sha Allah.

==================================

No comments:

Post a Comment