Thursday, 15 September 2016

Danladi Haruna -:|:- KAMANCECENIYA TSAKANIN NIJERIYA DA KASASHEN AMERIKA DA KENYA DA SENEGAL.

Danladi Haruna -:|:- "Ba kasar Nijeriya ce kadai ta yi yunkurin samun canji daga miyagun shugabanni ba, kuma ba ita ce kadai kasar da ta soma shiga cikin matsin tattalin arziki da fadin tashin shugabanni ba."
Danladi Haruna


Danladi Haruna, wanda sanannen Marubucin Littattafan Hausa ne musamman akan abubuwan da suka shafi Labaran Barkwanci da kuma ilimin Kwamfuta. Yana daya daga cikin Marubutan Littafin "Dare Dubu da Daya". A yau 15-09-2016 ya rubuta a Shafinshi na Facebook, inda yai bayani akan kamancexniyar dake tsakanin Nigeria da manyan kasashen ketare irinsu America, Kenya da kuma Kasar Senegal.






Danladi Haruna ya rubuta kamar haka:.
 "Ba kasar Nijeriya ce kadai ta yi yunkurin samun canji daga miyagun shugabanni ba, kuma ba ita ce kadai kasar da ta soma shiga cikin matsin tattalin arziki da fadin tashin shugabanni ba. Sai dai da dukkan alamu shugabannin kasar har yanzu ba su da nufin daukar darasi daga abubuwan da suka faru a wasu kasashen ballantana su iya fitar da A'i ga rogo. Zan dauki wasu abubuwan da suka auku a kasashen Amerika, da Kenya da Senegal domin kalato wani darasi da nake ganin ya dace shugabanni da talakawan kasarmu Nijeriya za su dauka domin samun nasarar abin da suka sa a gaba.
.
"A shekarar 2008 lokacin da Obama ya fito takara, kalmar canji ta zama ruwan dare ga kowa da kowa; canjin mulki daga farare zuwa bakake, canji daga matsin rayuwa zuwa walwala, canji daga yaki zuwa zaman lafiya da kuma canji da zaman banza zuwa ayyukan yi.
.
"A lokacin kuwa Obama ya tarar da kasar da fada cikin durkushewar tattalin arziki wanda aka ambata da 'great recession' wanda rabon da a samu irinsa fiye da shekara 70. A lokacin kudaden da ke zagayawa sun ja baya da kimanin kashi 5.1, fiye da mutane miliyan 12 sun rasa aiki, kamfanoni sama dubu 10 sun durkushe har ila yau kayan masarufi na kara hauhawa sakamakon wannan al'amari.
.
To amma duk da wannan ja'iba da shugaban ya tarar a kasar, bai tsaya yana ta romon baka ba, bai ci gaba da zargin shugabannin da suka gabata ba, kuma bai yi watsi da shawarwarin da masana ke ba shi ba. Ya yi tsayuwar daka wajen kawo canji kamar yadda ya alkawarta. Duk da yawan zanga - zanga da 'yan adawa ke yi, da zuga da turjiya daga 'yan majalisa, sai da ya samu nasarar aiwatar da dokar lafiya wadda aka fi sani da 'ObamaCare'. Ainihin dokar ana kiranta 'Patient Protection and Affordable Care Act' ta bayar da dama wajen karbar haraji daga manyan mutane domin a yi wa talakawa aiki ta fuskar lafiya da kula da gidaje. Kodayake, a shekarar 2014 an zabtare wasu abubuwa daga tanade-tanaden dokar, kuma a shekarar 2020 dokar za ta gama aiki, amma an samu gagarumin canji daga cikinta. Ta taimaka kwarai wajen farfado da tattalin arzikin Amurka wadda saura kiris ta fada cikin halin tsaka mai wuya.
.
"Gwamnatin Obama ta yi shiri da gaske wajen ceto manyan kamfanoni da suka doshi hanyar durkushewa. Cikin gaggawa aka ware dala miliyan 700 aka rarrabawa manyan kamfanoni ta karkashin wata doka da aka kirkiro mai taken 'American Recovery and Reinvestment Act' cikin shekarar 2009. Dokar ta tanadi samar da ayyukan yi da sana'a da kuma zuba hannun jari da inganta ilmi da kimiyya da fasaha.
.
"Koda yake Obama nasara bayan ya jajirce kuma ya murtsuke idonsa ya shafa masa toka. Ya gamu da cikas da dama musamman daga irin tanade - tanaden doka a kokarinsa na yiwa dokoki biyayya sau da kafa. Shi da kansa ya amince da cewa babban kuskuren da ya tafka a zangonsa na farko shi ne kokarin yi wa kowacce doka biyayya. Ya ce, "kuskurena a shekaru biyun farko shi ne tsammanin samar da dokokin da suke tafiya kan daidai. To amma yanayin ofishin nan yana fada wa Amerikawa cewa hadin kai da sadaukarwa ne kan gaba musamman a lokutan matsi." Har zuwa yanzu dai kasar Amirka na kaffa - kaffa domin gudun sake fadawa cikin wani matsin tattalin arzikin.
.
"Darussan da ya kamata mu dauka mu anan Nijeriya ya hada da, dole shugaba ya karbi shawarar masana kuma ya yi aiki tukuru ba tare da dora wa wadansu da suka gabata laifi ba. Misali, jam'iyyar PDP na dora alhakin tabarbarewar Nijeriya kan sojojin da suka shafe sama da shekaru 32 suna mulki. Zuwan APC kuma ta hau zargin PDP da suka yi shekaru 16 suna mulki. Watakila idan APC din sun kau su ma a rika zarginsu da cewa ragon azancinsu ne ya jawo lalacewar arzikin Nijeriya. Idan aka ci gaba da tafiya kan haka, babu wani abin ku - zo - ku - gani da za a samu.
.
"Dole ne kowa ya jajirce ya sadaukar da kai wajen samu ci gaban tattalin arzikinmu, ba aikin shugaba ne kadai ba. Hatta talakawa da sauran masu fada aji na da rawar da za su taka. Sai dai kalaman da wasu shugabannin kasar nan ke fada musamman ministoci, babu ma'ana ko kadan. Kalamansu daidai yake da rashin imani da tausayi da rashin lura da abin da ka je ya zo. Na tabbata kuwa idan haka za su ci gaba da aiwatarwa, saura kiris talakawa su dawo daga rakiyarsu.

A karshen Rubutun nasa ne yayi kira ga shuwagabannin dake rike da madafun iko, inda yake cewa:

"Ya kamata shugabannin nan da ke rike da madafun iko su yi koyi da darasin da aka samu a kasar Kenya. Zan zo da bayanin a rubutu na gaba."

Daga: Sani Hamza Funtua: Cliqq Magazine Hausa Editor.

No comments:

Post a Comment