Badakalar Naira Biliyan 18: Hukumar EFCC ta tabbatar da Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Shema, a matsayin wanda take nema Ruwa a Jallo.
Daga: Sani Hamza Funtua. Cliqq Magazine Editor.
Hukumar nan ta "Economic and Financial Crimes Commission", (EFCC) a daren ranar Laraba, ta tabbatar da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shema, a matsayin wanda take neman ruwa a Jallo, akan bacewar makudaden kudade har Biliyan 18 wanda suka bace daga Asusun hadin guiwa na Kananan Hukumomi.
Labari ya tabbata ga Cliqq Magazine cewa hukumar ta rattaba sunan tsohon gwamnan na jihar Katsina a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bayan da hukumar ta kasa riskar tsohon gwamnan a gidanshi dake a Aokoro don kamashi.
“Mun dade muna bibiyarshi da sa ido akanshi da zummar tabbayar da hukunci a kanshi idan muka tuhumeshi muka sameshi da laifin da ake zarginshi dashi. Sai dai da jami'anmu suka isa gidan nasa, sun taras baya nan.
“Maganar gaskiya anan itace hakurinmu ya Kare akan Ire-iren Uzurorin na tsohon gwamnan, wannan yasa kawai muka yanke shawarar mu sanyashi a matsayin wanda muke neman ruwa a Hallo, saboda sau tari munsha aika mashi da katin gayyata amma yana bamu uzurori da zasu hanashi amsa ayyatarmu," --Wani babba a cikin hukumar ta EFCC ya fada.
“Muna neman shi ne don yayi mana bayanin yadda ya salwantar da sama da Biliyan 18 daga asusun hadin guiwa tare banzatar da wadannan kudade, wanda hakan ya jawo tsananin rayuwa ga mutanen Jihar ta Katsina. Sai dai shi tsohon gwamnan yaki ya kawo kanshi don amsa wadannan tambayoyi" Babba a hukumar ta EFCC ya kara fadar hakan.
Shema dai shine wanda ya gaji mulki daga tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban Kasar Nigeria a shekarar 2007, sannan ya sauka a shekarar 2015, shine ya samu shaidar 'Gwamna mafi aiki' daga cikin gwamnonin jam'iyyar ta PDP sannan ya samu nasarori da dama a tafiyarshi ta siyasa.
An yabe shi da kafa manyan ayyuka a jahar tare da Samar da Manyan makarantu tun daga sakandire zuwa makarantun gaba da sakandire a Jihar, wanda ya habbaka ilimi a Jihar dama makwaftanta.
No comments:
Post a Comment