Saturday, 10 September 2016

Sanarwa | Sani Hamza Funtua Sabon Edita Na Cliqq Magazine Hausa



BAYANAI:
Suna:  Sani Hamza Funtua.
Adireshi:  Magajin Makera, Funtua. Katsina State.
Email:  
Oneheartbit@gmail.com
Lamabar Kira:  07032183026


TAKAITACCEN TARIHI

An haifi Sani Hamza Funtua a garin Daudawa, 10 ga watan Afirilu, shekara ta 1993. Yayi karatun Firmare a nan garin na Daudawa, ya wuce garin Bindawa inda yayi karatun Sakandire nashi. A yanzu haka Sani Hamza Funtua na karatu a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Jihar Bauchi.



Allah ya azurta Sani Hamza Funtua da baiwa ta Fasaha da Kirkira. A shekarar 2008 ya fara rubuta wakokin Hausa har yana rairasu, ya samu karbuwa musamman a wajen 'yan Siyasa da kuma bangaren nishadantarwa. Zuwa shekara ta 2010, ya fara rubuta littattafan Hausa duk da a lokacin bai samu damar bugawa ba. A yanzu, Sani Hamza Funtua yafi kwarewa a fannin kirkira da fasaha ta Rubutu.

Shine marubucin nan da wani dan Majalisa yasa aka kulleshi tsawan kwanaki Uku, ba don komai ba sai don tsoron kaifin alkalamin shi, sannan shine marubucin shahararren Littafin nan "KARSHEN MADIGO", wanda ya karade duniyar Yanar Gizo-gizo. Haka zalika, Sani Hamza Funtua marubucine na musamman dake iya rubutu akan ko wane Fanni, walau Siyasa, zaman-takewa, halin rayuwa da kuma kokarin yin Rubutu akan hanyoyin ci gaban Al'umma naki daya. Bugu da kari, yanzu haka yana daya daga cikin Marubuta Fina-finan Hausa masu tasowa da tauraruwarshi ta fara haskawa.

Ya zuwa yanzu, Sani Hamza Funtua bashi da aure, a cewar shi: "Kayi mata idan ka auri Karatu. Domin Ilimi shi zai zaunar da matarka tsawon rayuwa. Sannan Kayi mata bayan ka samu Shuhura, domin darajarka na tare da daukakarka, matarka kuwa zatafi zama bisa ga Nasararka."


Allah Ubangiji Ya Tayi Shi Riko

1 comment: