Monday, 12 September 2016

RIGAR DA BA WUYA : HASASHEN GYARA A SAKON BABA! Daga Kabir Sa'idu Bahaushe Dandagoro

Rigar da ba wuya ce na dunka,
Kowas saka ta daidai ya dace.
-Alh.Sani Sabulu Na-Kanoma a wakarsa ta 'Mai Dadaro'.
Da farko dai ina mika sakon barka da Sallah ga daukacin al'ummar Musulmi wanda Baba na cikinsu.


Ba tare da wata tankiya ba,na fara dinka riga marar wuyan nan da fatan kowane Baba ne zai saka ta,ta dace da shi don bukatata kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ina daya daga cikin wadanda suka saurari sakon Baba a Sallar da ta gabata da kyau matuka,kuma ma ni din nan Balan-gada ne Kan abubuwan da suka yi wadari bayan sakon Baba,har dai daga karshe abin ya zama wani babban wasan yara na katun da ya fusata jama'ar jihata matuka suka yi ta faman aman maganganu kamar duwatsu.


Wasu da yawa sun ce bai kamata Baba ya rika amfani da kakkausan harshe a sakonsa ba,kyau ace kokarin fadar abubuwan ci gaba ya yi ba bugewa da ba da labari ba na abin da ya gabata,tunda dai a ganinsu ba darasin Tarihi yake koyawa ba.


A cikin rigar nan da nake dinkawa,aljihunanta da na wandonta guda biyar ne baki daya,da hake nake son Baba ya cika su da abubuwa masu matukar muhimmmanci da zan kawo yanzu.
Aljihun gaba zan so ace ban hakuri aka zuba a cikinsa,kan maganganun baya da kuma yanayin da jama'armu suka samu kansu a ciki na kuncin rayuwa.


Aljihu na biyu kuwa,fatana Baba ya sanya batun ibtila'in kashe-kashen da laifuffukan fyade nan da suka yi warin dan duwale a jiharmu,abin ya dame mu matuka,kuma barazana ce mai girma sosai ga kwanciyar hankalin kowa Baba,za mu so sanin fari kuma kakkarfan matakin da ka dauka don ganin ba a yi kwalli da tabarya ba.

Batu na uku da ya kamata ya yi nauyi a aljihun rigar nan,shi ne batun inda aka dosa game da tattalin arzikinmu da ya zama kwai a cikin kwalba,tunda dai mun san akwai tushe to kuwa ya kamata a yi shuka mu ga 'ya'yanta da wurwuri duk da dai muna sara da duba bakin gatari ne.
Aljihu na hudu kuwa idan da hali a fada mana irin shirin da ke akwai nan gaba kan ci gaba mai dorewa ganin abubuwan Baba ba su fara kai wa ga ganin idanuwan mutane ba yadda ya kamata,sai a shata yadda za a yi babban taron masu ruwa da tsaki a dauki matakan gaggawa da wurwuri.




Aljuhu na biyar Baba ko da za ka sanya wayarka ciki da 'yan kudade a ciki to kuwa
zan bukaci ka dan sakaya batun zargin kayan mutuwar nan da ake ta batu,da kuma batun yadda wasu ta-bakin gafiyarka da suka nemi na goro,inda wata Hajiya ta banbara maganar kowa ya ji,don Allah a fidda jakai daga cikin duma kada su yi barna!

Ina maka fatan alheri da fatan cika aljihunanka da wadannan abubuwa na sama,don zan so a matsayinka na Baba idan muka hadu na ga nauyin aljihunan na fesa maka turare mai kamshi sosai,kuma tunda rigar ba mai wuya ba ce to nauyin abubuwan zai sa ta maka daidai ka yi kyau sosai.

Mu yi shagulgulan Sallah lafiya,bissalam.
Kwamared Kabir Sa'idu Bahaushe Dandagoro.
08038387516.


kabeerloquacious77@gmail.com.

No comments:

Post a Comment