Thursday, 1 September 2016

KYAWUN ALKAWALI CIKAWA BABI NA BIYU (2).-Comrade Dalhat Usd Danja

Kamar yadda kuka sani cewar mai girma Gwamna a lokacin yakin neman zabenshi yasha Alwashin Samar da ruwansha a fadin jahar katsina, Cikin Ikon Allah Mai girma Gwamna yana dafe madafun iko da wata ukku ya Maida hankalinshi ga wannan Alkawarin daya Dauka a Inda ya fara gyaran Dam din dake garin Malumfashi ruwa wanda ada kafin wannan gwamnatin ta hau Al'ummar Malumfashi suna da Matsalar rashin ruwan sha, zuwan Mai Girma Gwamna keda wuya aka gyara masu tashar Samar da ruwan sha Wanda yanzu haka ruwa ya samu a garin Malumfashi.

Daga nan sai Dam din Garin Jibia wanda wannan Dam din shike bama Al'ummar Jibiya da kewaye ruwa sannan kuma dashi suke amfani wajen yin Noman Rani zuwan mai girma Gwamna ya gyarashi yanzu haka wannan Dam din yana bada ruwa sosai fiye da yanda yake badawa.


Da Sai Babban Dam din Ajiwa wanda  yake bama Cikin Garin katsina da kewaye Ruwan sha, Shima wannan Dam din mai girma Gwamna ya ware kudi Domin gyaranshi wanda yanzu haka Aikin ya kai 70-80% Kuma nan bada dadewa ba wannan Dam Din zai dunga bada Ruwa akalla 1.3liter a kullum .

Kamar yanda kowa yasani Ruwa shine ginshikin Al'umma kuma Abokin Rayuwa Wannan gwamnatin tazo Domin Ceto Al'umma kuma ta kai Jaharmu Ga tudun mun tsira Munama Wannan gwamnatin Fatan Alheri # IndeedMasariIsWorking . 

Comrade Dalhat Usd Danja 01-09-2016

No comments:

Post a Comment