Hukumar jarabawar Kasa wato "National Examination Council (NECO) a ranar juma'ar data gabata ta saki sakamakon jarabawar daliban da suka zauna a wannan shekara ta 2016. Tare da kaso 88.51 na daliban sa suka zana jarabawar sun samu 5 Credit, Pass da kuma sama da hakan a darussan Turanci da kuma Lissafi.
Sanarwar ta fito daga hedikwatar hukumar dake Jahar Minna, Rijistaran na NECO Prof. Charles Uwakwe, yace: "An samu karuwar kokarin daliban wannan shekarar da kaso d'aya, idan aka hadasu dana shekarar 2015"
Uwakwe yace: " Makarantu 194 ne suka Shiva cikin sunayen makarantun da aka kama da laifin Satar amsa, inda makarantu 14 sun shiga cikin sunayen makarantun da Hukumar kula da jarabawar sukaki tantance sunayensu akan Satar jarabawa.
Ya nuna takaicin yadda karuwar makarantun da aka kama da laifin satar amsa suka yawaita, ya kara da tabbatar a cewa duk makarantar da aka samu da wannan laifi za'a cire sunanta. A hannu daya kuma ya nuna jin dadinshi akan yadda aka samu karuwar kokarin daliban a wannan shekarar da kuma kokarin da ma'aikatan hukumar ta NECO suka nuna.
Sannan ya tabbatar da cewa NECO ba zata rage daga kokarin inganta Jarabawar ba musamman a kokarn da takeyi yanzu na ganin ta samawa manya kyakkyawar shaida a idanun duniya.
Yace: " Ina so na nemi hadin kai da taimako daga dukkanin StakeHolder namu. Ya kamata a rika kallon NECO a matsayin wata karamar yarinya ta Nigeria [Nigerian Baby] wacce take bukatar kulawa da kuma tallafawa daga kowa don ganin ta cimma zama a jerin farko na samun babbar daukaka. A duniya. Muna Aiki tukuru don tabbatar da ta zama abin kwatance a fadin dubiya bama Nigeria kadai ba.
Uwakwe daga karshe yace, "Dalibai zasu iya duba sakamakon jarabawarsu akan Web-Site na NECO.
No comments:
Post a Comment