Sunday, 18 September 2016

NIJAR da CHADI sun Kashe Yan Boko Haram 38

Rundunar sojin Nijar ta ce dakarunta da hadingwiwar na Chadi sus kashe mayakan kungiyarBoko Haram talatin da takwas, a samamen dasuka kai a yankin Diffa dake kudu .


A cikin wata sanarwa, kakakin ma'aikatar tsarota Nijar, Kanar Moustapha Ledru ya ce sojojibiyu sun samu raununaka a samamen, wanda akakai bayan harin da mayakan kungiyar suka kai akauyen Toumour, dake kusa da tabkin Chadi.Kanar Ledru ya ce sojojin hadin gwiwar sunkuma kwace makamai masu yawa, da harsasaidaga wajen mayakan.

Ma'aikatar tsaron ta Nijar ta ce sojojin na cigaba da fatattakar mayakan kungiyar ta BokoHaram daga yankin.Sojojin sun kai samamen na hadin gwiwa ne atsakanin ranar Litinin zuwa Laraba a kauyukanGueskerou da Toumour, dake kudu masogabashin Nijar.

Wasu mazauna yankunan da kuma wata kungiyamai zaman kanta sun ce a ranar Laraba,mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai harigarin na Diffa, inda suka saci abinci damagunguna, amma ba su kashe kowa ba.

A watan Fabrairun 2015 ne Boko Haram din tafara kai hare-hare a yankin Diffa.A watan Yulin wannan shekarar, aka kafarundunar tsaro ta hadin gwiwa tsakanin Najeriyada Nijar da Chadi da Kamaru don kawar damayakan kungiyar ta Boko Haram daga kasashenRikicin Boko Haram na tsawon shekaru bakwai,ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane dubuashirin a Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar,sannan fiye da miliyan biyu da dubu dari shidasuka rasa gidajensu.

No comments:

Post a Comment