#ChangeBeginsWithMe
GASKIYA GAME DA WANNAN SHIRI.
GASKIYA GAME DA WANNAN SHIRI.
.
Da yawa daga masu tunani a Nigeria na tunanin cewa Nigeria na kan samun Garanbawul, kasar zata ci gaba da zama a matsayin Kasar da take kan samun ci gaba. Wani karatun kuma, cewa matsalar Nigeria a yanzu ta shugabanci wanda idan da za'a samar da kyakkyawan shugabanci to matsalolin da kansu zasu yi kaura daga cikin kasar. Nigeria zata ci gaba ne kadai idan ta danna malatsin malatsinanta mafita a dukkan matsalolinta, wannan ma wani karatun ne na daban. Wasu kuwa na tunanin cewa babu abinda kasar take bukata a yanzu illa manya-manyan makarantu da za'a koyar da ilimin Siyasa da kuma sanin tattalin arzikin kasa, don hakan ne kadai zai war-ware duk wata matsala dake kokarin kunno kai a cikin kasar.
A cikin dukkan wadan-can karatukan, wanda yayi magana akan Matsalar Nigeria itace shugabanci, yafi kama da matsalar da ke bukatar kasar ta latsa mashi malatsin kawo gyara akanshi. Domin kuwa shugabanci ne kadai wanda zai iya saukar da kalubale a bakin kofar shiga garin al'umma tunda dai al'ummar ce ke samar da komai har dasu manya-manyan makarantun da kuma shugabanci. A nan ya kamata ayi tunanin wanne ne zai gyara wanne: shin al'umma ce ya kamata ta gyara manyan makarantun tunda sune suka samar dasu, ko kuma manyan makarantun ne zasu gyara al'ummar tunda sune ke jan ragamar al'amuran su?
Idan muka duba a lokutan baya, gwamnatocin da suka shude sun sha kawo cibiyoyi daban-daban tare da shirya [Programmes] don ganin al'umma sun canja dabi'unsu ta yadda za'a cimma ci gaba na kasa gaba daya. Babu wanda zai ki yarda da irin rashin tarbiya da mummunar dabi'ar da ke yawo a cikin rayuwa da kuma tattalin arzikin kasarmu, amma duk da hakan; dukkan wadannan cibiyoyin ta kasa cimma burinta na samar da tarbiyar al'umma, karshe ma sai dai su disashe tare da gwamnatin don dama sune suka kirkire su.
Ita kuwa wannan sabuwar gwamnati da ake ganin tana yaki da rashin tarbiya itama ta hau sahun magabatanta. A kwanakin baya kadan ne, ta kirkiri wani sabon kamfe din nata na gyara tarbiyar mutane mai take #ChangeBeginsWithMe. Sai dai akasin haka, yan Nigeria suka fara sukar gwamnati akan hakan. Kamar yadda aka saba, tuhumar gwamnati akan ta fara canja tsarin mulkinta, kafin ta dawo tacewa mutane su canja.
Wasu daga cikin dalilan dake sawa Yan Nigeria suki amincewa da ire-iren wadannan [Programmes] din sune:
Dan Adam yana rayuwa ne a cikin al'ummar da ya samu kanshi a ciki, zayyi wuya ya iya canja tsarin rayuwarshi sabanin wacce ya riski kanshi a ciki. Kamar misali, Musulmai dake a arewacin Nigeria na yin azumin watan ramadana a cikin yanayin zafi, sannan za'aiya shafe kwanaki biyu babu ko kyallowar wuta a wasu garuruwan na arewa. A lokacin da aka zo shan ruwa, a lokacin da kowa ke neman wani dan abu mai sanyi ya sha, mutum zayyi mamakin ganin yadda ake kai-komo a wasu sassa cikin Jahar Katsina don samo Kankarar ruwan sanyi.
Dan Siyasar dake zaune cikin jama'ar da keda karamin hali, zai gina fan-fon tuka-tuka guda biyu a cikin gidanshi wanda hakan zai sa ko wane waje a makwaftanshi ruwansu zai janye. Sai ya gina masu wani fan-fon a bayan gidanshi sannan kowa dole a nan zaizo ya debi ruwa. Abin da takaici idan safiya tayi kaga yadda yara 'yan makaranta da kuma magidanta suna rige-rigen zuwa diban ruwan don tafiya wajen aiki da kuma makaranta. Wannan fa al'umma ce da take da ruwan fan-fo tun kafin shekarar 1999. Wani misalin kuma shine injin ATM. A jihar Katsina zaka taras da kadan ne ke aiki, sannan zaka taras basa iya biyawa kwastomominsu bukatansu, sannan ga daruruwan mutane daga ketaren kauyukan jahar, suma sunzo yin amfani da wannan Mashin. Samar da nutsuwa da kuma canji a irin wadannan wurare kusan abu ne da bazai iya yiyuwa ba.
A bangaren shari'a da kuma doka kuwa, masu madafun iko sun cusawa talakawa akida ta doka an kafa tane don talaka yabi shi kuma mai kudi ya karya. Masu kudi, har sai in sun aikata babban laifine kamar satar biliyoyin kudi daga asusun gwamnati, sunfi karfin hukuma da shari'a. Koda hakan ta faru, ana bayar dasu beli akan kudi miliyan daya, ko kuma suyi zaman wakafi na sati daya. Amma talaka kuwa zai sati kaza, idan yayi rashin sa'a aka kamashi to zai kare kusan rayuwarshi ne a gidan yari ba tare da bada beli ba. Samun karamin sabani da mai kudi zai sanya zuwan jami'an tsaro cike da mota don azabtar da talaka. Yayan masu kudi tare da na talaka zasu aikata laifi a tare, amma za'a saki dan masu kudin shi kuma dan talaka a turashi gidan yari. A can ne har zai rube ba tare da an sake shi ba.
Masu kafa hukunce-hukunce da ka'idoji sune har kullum ke kan gaba wajen karya wadannan hukunce-hukunce da ka'idoji. Su dai aikinsu samar da doka: Sune ke karya doka da ka'idojin Titi, suna yin tuki yadda suka ga dama, basa bin layi aduk wasu al'amura na al'umma. Mutum zai iya ganin motar jami'in Vehicle Inspection Officers (VIO) ko 'yan sanda a saman titi fitila a fashe, ko tayoyin da suka lashe, amma zaka gansu suna kama masu motocin haya da laifi irin nasu.
Jam'iiyar APC tayiwa 'yan Nigeria alkawari don haka ne ma aka zabeta, amma da suka hau madafun iko sai suka fara war-ware wadannan alkawura. A cewar wasu yan Nigeria, abubuwa da yawa suna dai ci gaba da tafiya kamar yadda suke a mulkin baya; kamar misali wajen bayar da aiki, wajen yaki da cin hanci da rashawa inda masu madafun iko ke cin hanci da rashawa amma suna azabtar da talakan da baici kamar yadda sukaci ba. A irin wannan yanayi yan Nigeria ke tunanin wancakalar da wannan canjin da suka kwata shekara daya data gabata.
Dukkan wadannan cibiyoyi ko [Programmes], gwamnati na kawo su a lokacin da bai dace ba. Kamar misalin wannan na #ChangeBeginsWithMe, a yanayin karyewar tattalin arziki da ake ciki da kuma matsi na rayuwa da talaka yake a ciki, kawo irin wannan shiri da kamar wuya ya samu karbuwa a wajen mutane. Bisa gaskiya ma, ba'a taba yiwa 'yan Nigeria irin wannan cin fuskar ba sai yanzu. Abin da kawai mutane zasu dora tunaninsu akai shine, APC ta gaza wajen cika alkawuranta don hakane ta kawo wannan shiri dazai juyar da tunanin mutane daga mantawa da wadancan alkawura.
Amma wannan ba yana nufin kada dan kasa na gari ya canja halayenshi ba, koda ace ba'a kawo ire-iren wadannan shirye-shiryen ba, da yawa daga cikin wasu dokokin ba'a karya su. Muna da sararin da zamu gyara kawunan a cikin kowane muke. Kamar karya doka ta zubar da shara ko ko ina, yin fitsari ko kashi a budadden waje, yin gudun da ya wuce ka'ida, sanya fastocin siyasa dana talla a saman alamomin titi, dukkansu abubuwane da ya kamata mu canja. Ni a wajena, Lallai CHANJI yana Farawa ne daga KAINA.
Daga: Baba Bala Katsina.
Fassara da Tacewa: Cliqq Magazine Editor.
No comments:
Post a Comment